PDP ta zargi APC kan tabarbarewar tsaro a Nigeria

Jam'iyyar PDP
Image caption Tun bayan shan kaye a zaben shekarar 2015, jam'iyyar PDP ke sukar mulkin APC

Jam'iyyar PDP ta gudnar da taron na nuna goyan bayan ga kokarin fitar da jam'iyyar cikin halin da ta shiga a matsayinta na babbar jam'iyyar adawa.

PDP ta yi hakan ne tare da goyan bayan gwamnoni da 'yan majalisar tarayya domin tabbatar dorewar dimokradiyar a kasar.

Tsofaffin ministocin babbar jam'iyyar adawa ta PDP a kasar sun zargi gwamnatin APC mai mulki da tarbarbara al'amuran tsaro da kuma sanya al'ummar kasar a cikin halin ha'ula'i.

Ministocin sun ce ba a taba ganin yadda satar mutane da yin garkuwa da su kamar a wannan gwamnatin ba.

A saboda haka suka yi kira ga gwamnati da ta kara a kokarin da ta ke wajen inganta lamuran tsaro.

A ranar litinin ne dai Minstocin suka shirya wani taro domin kokarin dinke barakar da ke jam'iyyar.

Ba wannan ne karon farko da jam'iyyar adawa ke zargin APC da aikata ba daidai ba a yadda ake tafiyar da mulkin kasar, ba wai kan batun tsaro kadai ba.

PDP ta taba zargi jami'yyar APC da hada baki da hukumomin tsaro wajen É—age zaben gwamnan jihar Edo da aka shirya yi, wanda hukumar zabe ta dage shi zuwa ranar 28 ga watan Satumba

Sai dai jam`iyyar APC a nata bangaren ta musanta, ta na cewa radadin faduwar zabe ne ke gigita PDP.

Labarai masu alaka