Nigeria ta cika shekara 50 da yakin Biafra

Al'umar Ibo a Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shekara 50 da yakin basasar Najeriya, amma har yanzu ba a daina jin radadin abubuwan da suka faru ba

An kwashe shekara 50 bayan yakin basasa na Biafra a Najeriya, inda har yanzu wasu 'yan kabilar Igbo ke kan bakansu na aware, yayin da wasu kuma ke son zaman kasar wuri guda.

An fara gwabza yakin ne, wanda aka shafe shekara uku ana yi, a ranar 6 ga watan Yuli na shekarar 1967 zuwa 1970, wato shekara 50 hamsin da ta gabata.

Yakin basasar da aka kwashe tsawon shekaru uku ana yi, tsakanin sojojin kasar da 'yan awaren Biafra a yankin Igbo na kudu-maso-gabashin Najeriyar ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi.

An yi kiyasin cewa sama da mutum miliyan uku ne suka mutu a lokacin yakin, yawancin su saboda tsananin yunwa.

Wani da yakin ya rutsa da ishi mai suna Mista Peter Adiole, ya shaidawa wakilin BBC yadda ya tsere daga harin bam a lokacin yakin, ya kara da cewa ''Da na tashi na daga kafa daya na kuma yunkurin daga daya kafar, sai na ga babu kafar da zan gusa sai kawai na zube a kasa''.

Wasu daga cikin wadanda aka fafata yakin basasar dasu a yankin Biafia, na ganin suna bukakar kafa kasar Biafia ta al'ummar Ibo, saboda abin da suka yi kirarin wai 'yan Najeriya na gallaza musu.

Kamar batun ya kwanta, a halin da ake ciki dai an sake yin wannan kiran kafa Biafra.

Tawagar BBC ta kai ziyara gidan Inamdi Kanu mai fafutukar kafa kasar Biafra, ya yi korafin cewa ba al'ummarsu na cikin halin kunci, babu wutar lantarki, babu tsaftataccen ruwan sha, sannan babu ayyukan yi.

Ya kara da cewa ''Hakurinmu ya kare, ba za mu iya ci gaba da rayuwa a haka ba, don haka mu ke so a ji ra'ayin jama'ar yankin kudu maso gabashin Najeriya kan batun kafa kasar Biafra.'.

A wani bangare kuma tsofaffi da wadanda suka shaida abinda ya faru a lokacin yakin basasar, sun bayyana fargaba kan abin da ka je ya zo ta fuskar hasarar rayuka da shiga halin rashin tabbas da aka tsinci kai a ciki a wancan lokacin.

Inda suka bayyana yakin na daya daga cikin mummanar abubuwan da mutum zai iya gani, a rana daya a kan kashe yara 50 zuwa 100, sai dai a binnesu a cikin rami daya. Wahalar da aka sha ta tsananta a lokacin yakin da ba a fatan a kara maimaita haka.

A halin yanzu, ra'ayoyin al'umman Ibo sun rabu biyu, yayin da wasu ke neman kafa kasar Biafra ,wasu kuwa sun fi mai da hankali a kan ci gaba da zama a Najeriya to amma su na bukatar a yi wa al'ummarsu adalci..