Sojojin Niger biyar sun mutu a wani sabon hari

Sojojin Nijar a bakin aiki Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jamhuriyar Nijar kamar makwabciyarta Najeriya na fusnkantar hare-haren masu tada kayar baya na Boko Haram

Rahotanni daga jamhuriyyar Nijar sun ce an kai hari a kan rundunar sojin kasar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar soji biyar a ranar Laraba.

Ko da yake kawo yanzu babu wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin kai harin, wasu rahotannin sun ce masu fafutukar addinin musulumci ne suka kai harin a yankin Tassara na jahar Tahoua.

An kai harin ne a kan wata rundunar soji da ke aikin tsaro a Midel da ke da iyaka da kasar Mali, inda nan ne 'yan tawayen Azbinawa ke shigowa kasar tare da kai hare-hare.

Wasu wadanda suka shaida lamarin sun shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa sun ga gawawwakin sojin kwance a kasa.

Rahotanni sun ce maharan suna da yawan gaske, dauke da manyan makamai, kuma an gwabza fada tsakaninsu da sojin Nijar da taimakon dakarun wanzar da zaman lafiya na Faransa da ke kasar.

A watan Oktoba da ya gabata ma dai, dakarun sojin Nijar 22 ne suka rasa ransu a wannan yankin sakamakon harin da masu tada kayar baya suka kai musu.