'An kwato Benghazi daga masu tsattsauran ra'ayi'

Libya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An samu fadece-fadace tsakanin bagarori biyu a rikicin Benghazi a wannan mako

Jagoran sojojin sa kai a kasar Libya, ya ce dakarunsa sun karbe cikakken iko da birnin Benghazi, bayan shafe shekara uku ana fafatawa da tsakaninsu da mayakan kungiyar IS.

Kwamandan dakarun sa kai da ke yankin mai cike da cece-kuce, Field Marshal Khalifa Hefter ne ya sanar da hakan ne a wani jawabin da aka watsa kai tsaye ta gidan talbijin.

Akwai rarrabuwar kawuna tsakanin sojoji da 'yan siyasa tun a shekarar 2014, abin da janyo kusan mafi yawan bangarorin kasar suka kasance babu kwakkwarar gwamnati, lamarin da ya janyo kungiyoyin masu dauke da makamai ke mulki.

Sanarwar ta zo ne bayan wata fafatawa a gundumar Sabri da ke Benghazi, lamarin da ya janyo zub da jini a wannan mako kuma ya yi sanadiyyar mutuwa tare da jikkata daga ɓangarorin biyu.

Rikicin Benghazi wanda aka kwashe tsawon shekara uku ana yi ya kasance tsakanin sojojin sa kai ƙarƙashin jagorancin Field Marshal Khalifa Hefter, da kungiyoyin masu fafutukar Islama daban-daban, ciki har da waɗanda suka nuna goyan baya ga ƙungiyar masu da'awar kafa daular musulinci ta IS.

A wani jawabin da aka watsa ta gidab talbijin, kwamanadan sojan sa kan mafi karfin iko a Libya, ya ce yanzu Benghazi ta shiga wani sabon babi na tsaro da zaman lafiya, da kuma sulhu.

Wasu hotunan da aka sanya a dandalin sa da zumunta sun nuna yadda wasu fararen hula a Benghazi da sauran sassan ƙasar ke bikin kawo ƙarshen rikici da ya janyo mutuwar mutane tare da lalata wani bangare mai girma na birnin wanda kuma ya sa dubban mutane suka rasa muhallansu a 'yan shekarun da suka wuce.

Amma kwamanda Hefter, na da abokan adawa da dama a cikin 'yan siyasa da sojoji a ƙasar.

Ba ya mutunta gwamnatin dake da goyon bayan ƙasashen waje da ke a babban birnin ƙasar, kuma ana yi masa kallon mutum ne mai buri babba ta fuskar siyasa da kuma soji.

Labarai masu alaka