'Takunkumi kan Koriya ta Arewa ya yi kadan'

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley ta ce takunkumin da ke kan Koriya ta Arewa ya yi kadan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley ta za a gabatar da sabon kuduri a majalisar kan Koriya ta Arewa

Jakadan China a Majalisar Dinkin Duniya ya shaidawa taron gaggawa da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniyar ya kira, cewa mai da martani ta hanyar amdani da karfin soji kan gwajin makami mai linzamin Koriya ta Arewa ba shi ne mafita ba.

Liu Jieyi ya kara nanata kasarsa da Rasha sun tattauna kan batun hana Koriya ta Arewa harba makami mai linzami da gwajin nukiliya.

Yayin da ta ke magana a taron kwamirtin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan gwajin makami mai linzamin da Koriya ta Arewa ta yi, Jakadiyar Amurkar a majalisar ta ce kasarta za ta yi amfani da karfin sojinta idan aka kai makura.

Nikki Haley ta kuma yi barazanar cewa Amurka za ta yanke huldar cinikayya da duk wata kasa a duniya da ta ci gaba da cinikayya da koriya ta Arewar. Inda ta ce za a mika wa majalisar wani sabon kuduri a kan Koriya ta Arewa.

Ms Helay ta ce harba makami mai linzamin da kasar ta yi a ranar Talata yana gaggauta rufe kofar lalama a kan batun.

Shi ma jakadan Faransa a majalisar ya goyi bayan Amurka kan batun sabon kudurin wanda zai kara karfafa takunkumi a kan koriya ta Arewa.

Koriya ta arewar dai ta yi gwajin makamin duk kuwa da haramcin da majalisar ta sanya mata.

Tun da fari dai shugaba Donald Trump ya soki kasar Sin kan huldar cinikayyar da koriya ta arewa, kuma a yau Alhamis ne ake sa ran zai sake yi wata ganawa da shugaba Xi Jinping a karo na biyu a birnin warsaw, kafin ya wuce zuwa birnin Hamburg inda za ayi taron kasashe karfin tattalin arziki na G20 a ranar juma'a, taron da ake sa ran shi ma zai tattauna batun gwajin makamin na koriya ta arewa.

Labarai masu alaka