Sama da mutane 400,000 ne ambaliyar ruwan Japan ta shafa

Sojoji na daga cikin masu aikin ceton
Bayanan hoto,

An aike da ma'aikatan ceto 7000 kudancin Japan

Ruwan sama da aka sheka kamar da bakin kwarya ya janyo ambaliyar ruwan a kudancin kasar Japan, inda ya tilasta sama da mutane dubu dari hudu barin muhallansu.

Tsananin ruwan da aka sheka ya shanye gine-gine masu tsaho ya yin da ya yi awon gaba da kananan gidaje, motoci na ta yawo a saman ruwa, lamarin ya fi munana a wurin shakatawar Kyushu.

Hukumomin kasar sun tabbatar da batan mutane 10, an kuma aike sama da jami'an dauki dubu bakwai dan taimakawa al'umar da lamarin ya shafa.

Masu hasashen yanayi sun ce an dade ba aga ambaliyar ruwa irin wannan ba, saboda baki daya yanayin ya sauya cikin kankanin lokaci.