Za a yi zanga-zanga gabannin taron G20 a Jamus

'Yan sandan kasar Jamus
Image caption An tsaurara matakan tsaron ne saboda masu boren na adawa da taron G20

An tsaurara matakan tsaro a birnin Hamburg na kasar Jamus, kwana guda gabannin fara taron kasashe masu karfin tattalin arziki wato G20.

Ana sa ran kungiyoyin agaji za su gudanar da zanga-zanga da safiyar yau, inda za su bukaci shugabanni su dauki mataki dan magance rashin daidaito tsakanin al'uma.

Akalla mutane dubu goma ake saran za su fito boren dan taruwa a birnin da kuma adawa da taron G20 da za a yi.

'Yan sanda sun yi gargadin kada masu zanga-zangar su tada tarzoma, inda sukai zargin sun samar da makamai a boye da za su yi amfani da shi ya yin boren.

Masu sukar lamari sun zargi jami'an tsaro kan rike manyan makamai, da nuna rashin jin dadi kan yadda aka yi amfani da ruwa wajen tarwatsa masu zanga-zanga a farkon makon nan.

Labarai masu alaka