Hotunan yadda wasu yankuna na duniya suke daga sama

Shafin intanet na Dronestagram ya bayyana sakamakon gasar daukar hotunan da aka nuna kwarewa kuma masu jan hankali.

An zabi dubban hotunan da aka dauka da kyamarar daukar hoto ta jirgi mara matuki a wannan gasar da Dronestagram ta ke shiryawa a kowace shekara, kuma bayan tantancewa, alkalan sun zabi wadannan da muke nuna muku.

A cikin alkalan akwai mataimakin shugaban mujallar National Geographic, Patrick Witty da editan hotuna na National Geographic na Faransa, Imanuelella Escoli da wata tawaga daga Dronestagram.

Ku kalli hotunan da suka yi nasara a fannoni hudu: Yanayi da Alkaryu da Jama'a da kuma Kwarewa.

Yanayi:

Hakkin mallakar hoto J COURTIAL
Image caption Wannan hoton wata gona ce da a ke noma fure mai kanshi na Lavender a yankin Provence na Faransa. Hoton da J. Kautilal ya dauka ya yi nasarar samun matakin farko a fannin noma da tsire-tsire. Ya ce "Na tafi Welsol da fatan samun wani hoto mai daukar hankali, ba irin na faduwar rana ba. Na san lokacin girbi ne, saboda haka sai na jira zuwan taraktoci masu girbin furen na Lavender, wanda na san zai dauki hankali idan na sami hoton."
Hakkin mallakar hoto FLORIAN
Image caption Florenian kuwa ya dauki hoton yadda ruwan tekun Greenland ke zama kankara ne da kyamararsu ta jirgi mai sarrafa kansa. Wannan hoton ne a ka zaba a matsayin na uku.
Hakkin mallakar hoto BACHIRM
Image caption Wannan hoton na nuna dogayen benayen birnin Dubai ne daga sama, wanda ya sami nasarar yin fice a rukunin Birane.

Alkaryu:

Hakkin mallakar hoto ALEXEYGO
Image caption Wannan hoton madubin benen Mercury City Tower ne da ke na birnin Mosko na kasar Rasha, inda yake nuna sauran benayen da ke kusa.

Jama'a:

Hakkin mallakar hoto MARTIN SANCHEZ
Image caption A rukunin Jama'a kuwa, Martin Sanchez ne yayi nasara da wannan hoton mai suna 'Karshen Layi'. Ya ce, "Ina nuna wuri ne da idan ka isa sai ka manta ina ne sama, ina ne kasa."
Hakkin mallakar hoto HELIOS1412
Image caption Wannan hoton na wata mata da ta nuna yadda ake wani noman fadama a yankin Mekong Delta a kasar Vietnam, wanda shi ne ya yi na biyu a rukunin Helioz.
Hakkin mallakar hoto FEELINGMOVIE
Image caption Wannan hoton shi ne na uku a rukunin hotunan Jama'a. Hoton daga Fillingmu yake, kuma yana nuna yadda a ka binne wani mamaci a lokacin hunturu a birnin Cilio da ke Cantabria a Spaniya.

Kwarewa:

A bana an kirkiro wani sabon rukuni domin karrama kwarewar mambobin kungiyar Dronestagram.

Hakkin mallakar hoto MACAREUXPROD
Image caption "Ni da kawayena mun kusa zama iyaye, domin wannan ne na dauki wannan hoton don nunawa 'yan uwa da abokai yadda nake kallon abin." Hoton ya fito ne daga Thackeral na Macarieu Productions.
Hakkin mallakar hoto RGA
Image caption Wannan hoton da a ka dauka na zane a bisa yashi shi ma ya sami yabo.