'Jima'in baka yana jawo ciwon sanyi mai wuyar magani'

Kwayar cutar Sanyi
Image caption Hukumar WHO ta ce kwayar cutar yaduwa take cikin sauri kuma kwayoyin cutar suna bijirewa magani

Jima'i ta baki yana jawo mummunan ciwon sanyi kuma rashin amfani da kwaroron roba yana taimakawa wajen yaduwar cutar cikin sauri, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana.

Hukumar ta yi gargadin cewa ciwon sanyi (ko Gonorrhoea) yana da wuyar magani ko kuma ma ba shi da magani kwata-kwata.

Cutar wadda ake kamuwa da ita ta hanyar saduwa tana bijirewa magani cikin sauri.

Cututtukan makogwaro

Cutar sanyi tana shafar al'aura ce da uwar hanji da kuma makogwaron wanda yake fama da ita.

Sai dai yanzu batun yadda take shafar makogwaro ne jami'an kiwon lafiya suka mayar da hankalinsu a kai.

Dokta Teodora Wi ta hukumar lafiya ta ce idan mai fama da ciwon ya sha magani hakan ka iya jawo kwayoyin cutar Bacteria su kama makogwaro wadanda kuma suke bijire wa magani.

Ta ci gaba da cewa: "Idan aka yi amfani da magunguna wajen maganin ciwon makoshin hakan yana sa kwayoyin Bacteria su hadu da halittar Neisseria da ke makogwaro inda suke bijirewa magani."

Idan ana jima'i da baki da wanda yake dauke da ciwon sanyi, hakan zai bai wa kwayoyin Bacteria damar kai wa ga makogwaro kuma sai su kawo mummunar ciwon sanyi ko gonorrhoea, kamar yadda ta ce.

"An fara ganin matsalar kwayoyin cutar suna bijire wa magani ne a tsakannin wasu maza 'yan luwadi a Amurka," in ji ta.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Masana sun yi gargadin cewa yanayin yana da ban tsoro saboda yadda ake kirkiro magunguna kadan don magance cutar.

Hukumar ta yi nazari ne a kasashe 77 wanda sakamakon binciken ya nuna cewa cutar tana bijirewa magunguna.

A kalla mutane miliyan 78 suke kamuwa da ciwon sanyi wanda yake jawo matsalar rashin haihuwa.

Labarai masu alaka