G20: Dubban masu bore sun yi zanga-zanga

Jami'an tsaro da masu bore a birnin Hamburg na kasar Jamus Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yadda ake fesawa masu zanga-zanga ruwa kenan domin tarwatsa su

An tsaurara matakan tsaro a birnin Hamburg na kasar Jamus, inda za a fara gudanar da taron manyan kasashe masu karfin tattalin arziki wato G20.

Wakilin BBC ya ce dubban masu zanga-zanga da dubban jami'an tsaro ne suka cika tituna, inda suke jifan 'yan sandan kwantar da tarzoma da duwatsu da kuma kwalabe, yayin da 'yan sanda kuma ke harba musu hayaki mai sa hawaye da fesa musu ruwa don tarwatsa su.

Batutuwan da suka shafi kasuwanci da sauyin yanayi da gwajin makamin da Korea ta Arewa ta yi su ne za su mamaye taron na ranar Juma'a da masu sharhi ke ganin za a samu rarrabuwar kawuna a tsakanin shugabannin.

Daya daga cikin abubuwan da za a sanyawa idanu shi ne haduwar keke da keke a karon farko da za a yi tsakanin shugaba Donald Trump da Vladimir Putin na Rasha.

An dai shafe tsawon dare ana bata kashi tsakanin masu zanga-zanga da 'yan sandan kwantar da tarzoma.

A ranar Juma'a ne kuma ake sa ran kungiyoyin ba da agaji za su yi tasu zanga-zangar, inda za su bukaci shugabannin su kara hobbasa wajen magance matsalar rashin daidaito a tsakanin al'umma.

Labarai masu alaka