Dan Masani na cikin wadanda suka fi iya Turanci – Osinbajo

Mukaddashin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo tare da iyalan marigayi Dan Masanin Kano Hakkin mallakar hoto Nigerian Government
Image caption Shugabanni da sauran jama'a na cigaba da kai ta'aziyya gidan marigayi Dan Masanin Kano Alhaji Yusuf Maitama Sule

Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce ba ma Najeriya da Afirka ba, har duniya ta yi babban rashi a sanadiyyar mutuwar Dan Masanin Kano Alhaji Yusuf Maitama Sule.

Mista Osinbajo ya yi wadannan kalaman ne a fadar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Biyu a ranar Alhamis lokacin da ya je domin yin ta'aziyyar marigayin wanda ya rasu a wannan makon.

Ya ce Najeriya ta yi rashin wani babban mutum da kodayaushe burinsa shi ne ya hada kan kasa.

Ya ce, "Na taho Kano ne domin na yi muku ta'aziyyar rashin babban dan kishin kasa, kuma uban kasa, wanda babban jagoran al'ummar Najeriya ne."

Ya kara da cewa ya fara haduwa da marigayin ne "tun ina da shekara 15 da haihuwa. A wancan lokacin yana rike da mukamin minista kuma ya bayar da wata lacca a sashnin John F. Kennedy [na Jami'ar Harvard].

Tun daga lokacin nake bibiyar rayuwarsa ta siyasa."

Karanta karin bayani kan wannan da ma sauran labarai

Sunan Maitama Sule ya yi fice saboda kwarewarsa da iya magana da basira. Ba ya bata lokaci wajen bayyana matsalolin dake damun kasar nan da kuma hanyoyin gyara su", in ji Osinbajo.

"Yana daga cikin wadanda suka fi kwarewa wajen magana da harshen Ingilishi, kuma a rayuwata ban hadu da irinsu da yawa ba a duniya."

A nasa bayanin, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na Biyu ya ce "Mun yi rashin Dan Masani a daidai lokacin da kasar nan ke matukar bukatar mutane irinsa masu kira da a zauna lafiya, a hada kan jama'a kuma a mutunta addinan juna".

Dubban 'yan kasar ne suka halarci jana'izar marigayin, wanda ya rike manyan mukaman siyasa da dama a kasar, bayan rasuwarsa a wani asibiti da ke Masar bayan gajeriyar rashin lafiya.