Niger: An cafke mutane 15 kan kashe dorinar ruwa

Dorinar ruwa a Niger Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dorinar ruwa a Ayarou ta Jihar Tillabery

A kalla mutane 15 ne hukumomin yankin Ayarou a jihar Tillabery ta jumhuiriyar Nijar da ke yammacin kasar suka kama kan kashe wata dorinar ruwa.

Mutanen dai sun ce dorinar na barazana ga rayukansu da kuma na dokiyoyinsu.

Dorinar da aka kashen na yin ta'annati ne ga al'barkatun noman a gonakin manoman yankin da ke bakin kogin kwara a kasar ta Nijar.

Haka kuma ta na hallaka shanun jama'ar yankin.

Ta kuma hana jiragen ruwa yin shawagi a kan kogin Isa wato kogin Kwara.

Dorinar ruwa dai na daya daga cikin irin dabbobin da ke da kariya ta kar da a harbesu ko kuma a musgunamasu a hukumance a kasar ta Nijar.

Saboda da haka dokar kasar ta haramta hallaka irin wadannan dabbobi ko kuma yin barazana ga rayuwar su.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption garken dorina a Nijar

Garin na Ayarou dai inda lamarin ya gudana na da nisan kilomita 200 daga Yamai babban birnin kasar ta Nijar zuwa iyaka da kasar Mali.

Kuma wuri ne da ke samun ziyartar turawa 'yan yawon bude ido saboda su dauki hotuna da kuma ga yadda dorinar take ido-da-ido.

Kuma ya na daya daga wuraren da ruwa ke da zurfi ta yadda dorinar ke samun wurin zama wadatacce.

A shekara ta 2014 dorinar ta kashe dalibai 'yan makaranta guda 12 , da mata 7, da maza 5 masu shekaru 12 zuwa 13, a lokacin da ta kai farmaki kan wani jirgin ruwa samfurin kwale-kwale a kan kogin na Kwara a kauyen Libore da ke kusa da birnin Yamai kafin jami'an tsaron gundun daji su hallaka ta.

Haka a shekara ta 2013 jami'an hukumar gandun daji sun kashe wata dorinar bayan da ta ciji wani matashi a Yamai abun da ya yi sanadiyar mutuwar shi har lahira.

Dorinar ruwan dai ta na kasancewa mai fada da keta a lokacin da take biki ta na tare da jariranta.

Shi ya take kai hari ga jama'a da kuma sauran dabbobi.

Labarai masu alaka