Wutar daji daga Canada ta ketara jihar California ta Amurka.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gobarar daji

Wutar daji ta kama yankuna kusa da dari biyu a bangaren yammacin Canada, sashen British Columbia.

Wannan kuma ya sa hukumomin yankin kafa dokar ta-baci a karon farko cikin shekaru 14.

Tun da farko dai wutar ta fara ne sanadiyar tsawa a lokacin wani gagarumin hadari.

Ana nuno hotunan torokon harsunan gobarar suna lakume wasu bangarori na gandun dajin.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption gobarar daji ta manaye yankuna

Duban jama'a ne aka kwashe daga gidajen su.

Iska mai karfi da tsagwaron tsananin zafin wuta na haifar da cikas ga kokarin masu kashe gobarar.

Ita dai wannan wutar daji da ta mamaye yammacin Canada ta kuma ketara har zuwa jahar California ta Amurika , inda yanzu haka dumamar wutar ta sa zafin yanayi wurin ya kai sama da maki 40 ka maunin Celsius a wurare da dama .

Yan kwana kwana sama da dubu 2 ne ke ta kokarin kashe wutar.

Wannan gobara na faruwa bayan shekaru 5 na fari da yankin ya fuskanta, kuma wani ruwan sama mai karfi ya yi sanadiyar bazar da kuncin bishiyoyin dajin abun da ya sa wutar na ruruwa kamar ana zigata da zuga-zugai.

Hukumomi sun sanar da jama'a cewa yanayin zai ci gaba da kasancewa hakan har zuwa karshen mako.

Labarai masu alaka