Fasto: Baikon dala kawai nake so

Wani mutum na kirga dalar Amurka Hakkin mallakar hoto Getty Images

Limamin cocin Angalika na majalisar kasar Yuganda ya yi kira ga mabiya addinin kirista da su rika bayar da sadakar dalar Amurka da fam na Ingila a maimakon kudin kasar watau Shillings, in ji jaridar Daily Monitor mai zaman kanta.

Rabaran Cannon Christine Shimanya ne ya fadi haka a lokacin wata lacca da ya gabatar ranar Lahadi a cocin Namugongo Martyrs da ke birnin Kampala.

"Wasu mabiya addinin kirista na samun dala da fam a sanadiyyar halartar tarurruka a kasashen waje; kuma kamata ya yi su kawo dalolin da fam din a maimakon su rika sauya kudin zuwa shilling. Ku kawo dalolin nan da fam din, domin Ubangiji na bukatar su."

Wani limamin coci, Canon Henry Ssegawa, ya goyi bayan wannan kira da Rabaran Shimanya ya yi, inda yake cewa cocin na bukatar kudade masu karfi sosai, in ji jaridar ta Daily Monitor.

Labarai masu alaka