Dangote ya sasanta tsakanin Hausawa da Yarbawa

kamfanin Dangote ya raba wa wasu matasa takardun bada tallafi
Image caption Matasa za su samu tallafi daga kamfanin Dangote

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu da Basarake Oba na Ife, Oba Enitan Adeyeye Ogunlisi, sun kulla yarjejeniyar samar da zaman lafiya a tsakanin kabilun Hausawa da Yarbawa da ke garin na Ile-Ife.

Zaman dai ya zo a karkashin gidauniyar Dangote da ta bayar da sama da naira miliyan 50 ga al'ummar da rikicin kabilancin tsakanin Hausawa da Yarbawa ya shafa cikin watan Maris na bana.

Shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote na cikin masu halartar wannan taron sasantawar, inda ya bayar da wani tallafi ga matasan.

Sama da mutum 30 ne suka rasa rayukansu da kuma salwantar dukiya ta miliyoyin naira.

Sarkin Kano ya ce, "Mun zauna mun yi lissafi ni da Ooni da Dangote, mun ga cewa Hausawa sun yi asarar miliyan 35, Yarbawa kuma miliyan 15, kuma gidauniyar Dangote ta bai wa ko wannensu cek na banki don karbar iya abin da mutum ya yi asara.

"Mu dai yanzu haka addu'a za mu ci gaba da yi don kare afkuwar irin haka a gaba, kuma gaskiya Oni ya yi kokari wajen ganin an shawo kan matsalar a kan lokaci. Haka ya kamata shugabanni su dinga yi," in ji Sarki Sunusi.

Alhaji Abubakar Mamuda Madagali, shi ne sarkin Hausawan Ile-Ife, ya kuma yi kira ga hukumomi da su taimaka wajen gyaran gidaje da shagunan da suka salwanta a sakamakon rikicin.

"Gidajenmu sun fi karfin mu gyara da kanmu. Abin bakin ciki ma shi ne ba a saka gidajenmu a cikin masu bukatar taimako ba, domin a lokacin ina asibiti."

Amma ya ce a halin yanzu zaman lafiya ya dawo tsakanin mazauna garin, "muna zaune lami lafiya, ai kaga yadda muka rika gaisawa da hakiman garin. Da babu zaman lafiya, ai ba zamu gaisa ba."

Image caption Matasa za su samu tallafi daga kamfanin Dangote

A wajen taron, kamfanin Dangote ya raba wa wasu matasa takardun bayar da tallafi.

Da wakilin BBC ya tambayi wata mata 'yar kabilar Yarabawa a garin na Ile-Ife, Malama Rashida mu'amalarta da Hausawa ta fannin kasuwanci, ta bayyana cewa, "Alhamdulillahi, muna ci gaba da samun zaman lafiya fiye da zato. Ba wani fada, mu'amalarmu na tafiya daidai yadda ya kamata".

Ta yi kira ga shugabannin garin da su taimaka masu, "domin kasuwancinmu, da yanayin zaman lafiya ya dawo yadda muke so".

Labarai masu alaka