'Yan Boko Haram sun kai hari wajen zaman makoki

Jami'an kai daukin gaggawa a bakin aiki
Image caption Mutane 12 aka hallaka a lokacin da suke zaman makoki

Kungiyar Boko Haram ta kai harin bama-bamai a wurare daban-daban a birnin Maiduguri, harin da ya jawo mutuwar mutane a kalla 12 kuma 23 sun jikkata.

An kai harin ne a ranar Talata, inda biyu daga cikin maharan suka kai harin kusa da wani shingen da 'yan kato da gora suka kafa domin duba masu shige da fice.

Wata budurwa a cikin maharan ta lallaba zuwa kusa da shingen inda ta tayar da bama-baman da ke jikinta wanda ya yi sanadin mutuwar mutum uku.

Wata maharar kuwa ta tashi nata bam din ne kusa da shagon wani mai shayi inda wasu 'yan kato da gora da mutanen gari ke cin abincin dare.

Daga baya kuma, a wani wuri da jama'a suke zaman makokin wadanda suka rasa rayukansu a sanadiyyar hare-haren, wata 'yar kunar bakin wake ta fada cikinsu, inda ta tashi bam din da ke jikinta, kuma wannan harin ya janyo mutuwar mutane da dama.

An sami jimillar hare-hare guda hudu, inda mutane da dama suka jikkata.

Hare-haren na zuwa ne a daidai lokacin da a jami'an gwamnatin Najeriya za su ziyarci jami'ar Maiduguri domin tantance yawan asarar da hare-haren suka janyo.

Wannan harin shi ne na baya-bayan nan a cikin jerin hare-haren da kungiyar Boko Haram ta kai a birnin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Hukumar bayar da taimakon gaggawa ta jihar Borno da jami'an 'yan sanda sun ce yawancin wadanda a ka kashen 'yan kato da gora ne.

Daya daga cikin wuraren da a ka fi kai wa hari a bana shi ne Jami'ar Maiduguri.

A dalilin haka ne jami'ar ta fara haka wani rami mai tsawon kilomita 27 da zai zagaye jami'ar.

Labarai masu alaka