'Masu fuska biyu a gwamnatin Buhari ne kuraye'

Shehu Sani
Image caption Batun dai ya janyo cece-kuce a Najeriya, inda wasu ke ganin bai kamata a kira mutane da dabbobi ba

Cece-kucen da kalaman sanata Shehu Sani ya wallafa a shafinsa na facebook na ci gaba da daukar dumi, musamman ganin uwar gidan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wato Aisha Buhari ta yi amfani da hakan wajen maida martani ga 'yan kasar.

Wasu dai sun fusata da kiransu kananan dabbobi da Sanatan ya yi, inda shi kuma abin da ya ke nufi da hakan shi ne talakawa. Sai dai ya ce sun yi masa mummunar fahimta ne.

A wata hira da Sulaimanu Ibrahim Katsina na sashen Hausa, sanatan ya ce ya yi wannan shagube ne bi sa la'akkari da hujjojin da ya ke da su da za su kare kalaman da ya wallafa din.

Na farko sanatan mai wakiltar Kaduna ta arewa ya ce, yawan addu'o'in da ake yi kan Allah ya bai wa shugaba Buhari lafiya ya ragu matuka, idan aka kwatanta da lokutan baya musamman lokacin da ya fara zuwa asibiti.

''Akwai bangaren talakawa da ke masa addu'ar samun sauki da kuma dawo wa lafiya, to amma manyan 'yan siyasa su na nan su na kulle-kulle, da munafunci sun kasa zaune sun kasa tsaye.

A baya can sosai ake kare muradin shugaban amma yanzu kowa ya ja gefe ba sa cewa uffan, akwai mutanen da suke zagin shugaba Buhari kan wasu batutuwa.

Misali idan ka dauki sukar da ya sha a kan sakon barka da sallah da ya aike wa 'yan kasar ta nadar muryarsa, an yi ta cece-kuce a kan hakan dan me shugaban kasar zai yi magana da Hausa.

A wannan lokacin duk wadanda ka ke ganin su na zakalkalewa da son zama 'yan sahun gaba a wurin shugaban sun yi shiru babu wani daga cikin su da ya yi kokarin kare shi'', inji Sanata Shehu Sani.

''Wannan dalili ya sa na kira su da Dila ko Kuraye, su kuwa kananan dabbobi da suka dogara ga sarki Zaki dan kwato musu 'yanci su ne talakawa da sukai ammana da cewa ba za a hada kai da shugaba Buhari wajen tauye musu hakki ba''.

Ya kuma ce bai yi mamaki ba da uwar gidan shugaban kasar, ta maida martani kan shaguben da ya yi wanda ta ce Allah ya amshi addu'ar talakawa kuma nan ba da jimawa ba wanda akai domin shi zai komo gida.

Ya kara da cewa ''Daman ita ai uwa ce da kowa ya san ta da akida da tsage gaskiya, ba ta da tsoro, a baya ai ta taba yin magana akan irin wadannan mutanen.

Aka yi ta zagin ta da maganganu kala-kala, amma daga baya ai gaskiya ta yi halin ta dan kuwa su ne dai mutanen da ta ke magana akai da ba sa kare sunan shugaba Muhammadu Buhari, kowa son kai ya masa yawa''.

Labarai masu alaka