Lauyan de Silva ya ce za su daukaka kara

Luiz Inacio Lula de Silva
Image caption De Silva bai amince da hukuncin da kotun ta yanke ma sa ba, dan hakan zai daukaka kara

Lauyoyin tsohon shugaban kasar Brazil, Lula Da Silva sun ce za su daukaka kara kan hukuncin zaman gidan kaso na shekara tara da rabi da aka yanke masa bisa laifin karbar rashawa da cin hanci.

An dai sami tsohon shugaban da laifin karbar na goro ta hanayar karbar gida a bakin ruwa da kudinsa ya kai sama da dala miliyan daya wanda kamfanin gine-gine na OAS ya ba shi domin samun kwangila mai tsoka.

Daman dai shugaban jam'iyyar da Lula yake, Carlos Zarattini ya bayyana hukuncin da bita-da-kullin siyasa.

Mataimakin shugaban Jam'iyyar Workers Party Joao Daniel ya ce bai ga dalilin da za a yi ta kwan-gaba-kwan-baya ba kan shari'ar da sun san Lula ba shi da laifi ba.

Shi kuwa Jose Medeiros na jam'iyyar PSD ta hannun damar jam'iyyar Conservative ya ce gaskiya ce ta yi halin ta, ba wai ina nufin za mu yi ta shagalin murna ba ne, ya zargi mista de Silva ta janyowa kasar koma baya ta fuskar tattalin arziki, saboda cin hanci da rashawa da ya yi yawa tsakanin jami'an gwamnati.

An dai samu Inacio Lula de Silver da laifin karbar na goro kusan dala miliyan 3 da dubu 700, daga hannun wani kamfanin gine-gine OAS , dan a taimaka ma sa samun kwangilar babban kamfanin mai na kasar Petroleo Brzsileiro da aka sani da Petrobras.

Zargin da ya sha musantawa, ba dai shi kadai danbarwar ta shafa ba har da tsohuwar shugabar kasar Dilma Rouseff da shugaba mai ci Michel Temer da shi ma aka fara tuhumarsa a farkon wannan watan.

Labarai masu alaka