Kaspersky na Rasha ya musanta aiki da hukumar leken asiri

Shugaban kamfanin Kaspersky, wato Eugene Kaspersky

Wani kamfanin tsaro mai mazauni a birnin Moscow ya musanta zargin ya yi aiki tare da hukumar leken asirin kasar, bayan zargin aikata hakan da kafafen yada labaran Amurka da gwamnati suka yi.

Shafin internet na Bloomberg ya rawaito cewa ya ga sakwannin email da ke nuna kamfanun Kaspersky ya samarwa hukumar leken asirin kasar bayanan.

Kuma a ranar talata ne gwamnatin Amurka ta cire sunan kamfanin daga jerin sunayen wadanda aka amince ayi mu'amala da su.

Sai dai kamfanin shugaban kamfanin Kaspersky Eugene Kaspersky ya dage cewa ba shi da wata boyayyar mu'amala tsakanin sa da gwamnati.

Kaspersky ya yi kaurin suna wajen cire kwayar cutar da ke kama Kwanfiyuta, da samar da tsaro da kare abokan huldarsa.

Shafin Bloomberg ya sake kare batun sakwannin email da aka yi musaya tsakanin manya da kananan ma'aikatan kamfanin Kaspersky, da ke nuna yadda aka samar da wata kariya ta musamman ga hukumar leken asirin kasar Rasha.

Mista Kaspersky ya ambaci wasu abubuwa da suna ''Yadda za ka kare kan ka daga msu kai wa kwanfiyuta hari'', an kuma aike sakwannin emai din ne ga hukumar leken asirin Rasha.

Shugaban kamfanin Kaspersky ya ce abin damuwar shi ne masu satar bayanai ka iya amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba.

Sai dai mista Kaspersky ya nanata cewa kamfaninsa bai taba taimakawa wata gwamnati a fadin duniya da abinda ya shafi satar bayanan sirri na internet ba, kuma ba zai taba yin hakan ba anan gaba.

Bayan zaben shugaban kasa da aka yi a kasar Amurka, an yi zargin Rasha ta taimakawa shugaba Donald Trump yin nasara ta hanyar kutse cikin kwanfiyutocin hukumar zabe.

Sai dai kuma a wata hira da akayi da shi a gidan talbijin din kasar na NBC, Mr Trump ya ce ba bu wani abu tsakanin sa da Rasha,kuma ba wata huldar kasuwanci tsakaninsu.

Labarai masu alaka