Shugaba Jammeh ya yi sama da faɗi da kudaden Gambia

Yahya Jammeh Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Da fari shugaba Yahya Jammeh ya amince da shan kayen da ya yi, har ya kira Mista Barrow ya taya shi murna, amma daga bisani ya ki amincewa lamarin da ya shigar da kasar cikin tashin hankali

Shugaba Yahya Jammeh ya saci kudin kasar Gambia da ta kai dala miliyan 50- a lokacin da yake barin kasar.

Ministan shari'ar ya ce tsohon shugaban, Yahya Jammeh ya saci a ƙalla dala miliyan 50 na ƙasar kafin ya bar Gambia a watan Janairu.

An zargin Mista Jammeh da janye kuɗaden ta kamfanin sadarwa na ƙasar.

A halin yanzu, kotu ta sa hannu a kan sauran dukiyarsa da ke Gambia.

Mista Jammeh ya sha kayi a zaɓen shugaban ƙasa a watan Disamba, inda ya amince ya sauka daga mulki bayan da ƙasashen Afrika ta yammacin duniya suka yi barazanar cire shi da karfin soji. Inda ya nemi mafaka a Equatorial Guinea bayan kwashe shekaru 22 yana mulki.

Akwai rahotanni cewa jirgin saman da Mista Jammeh ya bar ƙasar da shi, na dauke da motoci da wasu abubuwa da dama.

Ministan harkokin cikin gida, Mai Ahmad Fatty, a lokacin da yake mai taimakawa shugaban kasar Adam Barrow da farko ya ce ya saci fiye da dala miliyan 11.

Amma a ranar Litinin, Ministan Shari'a ,Abubacarr Tambadou ya ce Mista Jammeh ya janye dala miliyan 50 tsakanin shekara 2006 zuwa shekara 2016.

Ya kuma zargi Mista Jammeh da ba da umurni cire kudaden daga babban bakin ƙasar.

Tun lokacin da Mista Jammeh ya bar ƙasar Gambia dai, bai taba hulda da wani ba haka kuma bai mayar da martani akan zargin ba.

Labarai masu alaka