Kwalara 'ta kama' ministocin Kenya

Mutane sun kamu da Cholera a wajen wani taro a Kenya
Image caption Mutane sun kamu da Cholera a wajen wani taro a Kenya

Hukumomi a kasar Kenya sun ce an samu rahoton mutum 33 sun kamu da cutar Kwalara ciki har da ministocin kasar biyu a babban birnin kasar Nairobi.

A ranar Juma'a, kafofin yada labaran kasar sun ruwaito cewa an kwantar da wasu ministocin kasar guda biyu a wani asibiti bayan sun ci wani abinci a wajen wani taro da aka yi.

Sai dai ba a tabbatar da cewa ko kwalara ba ce ko kuma cin gurbataccen abinci ne ya janyo aka kwantar da su ba.

Ko a watan da ya gabata ma, mutane da dama sun kamu da cutar kwalara a kasar bayan sun halarci wani taro akan lafiya a wani otel da ke birninNairobi.

Labarai masu alaka