An kashe masu yawon bude idanu 'yan kasar Jamus a Masar

Wadanda suka samu rauni na karbar magani a Asibiti Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Jami'an 'yan sanda sun ce suna bincike a kan dalilin da ya sa mutumin ya kai wannan hari kan masu yawon bude idanu

Wasu masu yawon idanu mata biyu 'yan kasar Jamus sun mutu, bayan wani mutum ya caka musu wuka a wajen wani wurin shakatawa a gabar teku da ke Hurghada a kasar Masar.

Akalla wasu mutum hudu kuma sun ji raunuka, bayan mutumin ya yanke su da wuka.

Tuni dai aka kama mutumin inda 'yan sanda ke masa tambayoyi domin gano dalilin kai harin.

A bara ma an kai hari wajen shakatawar inda har aka raunata masu yawon bude idanu biyu.

Masu ikirarin jihadi dai na kai hare-hare wuraren shakatawar kasar domin durkusar da hanyar samun kudin shigar da kasar ke dogaro da ita.

Labarai masu alaka