An kafa layukan sayen halastacciyar tabar wiwi

Ana tantance mutane kafin a sayar musu da wiwi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana tantance mutane kafin a sayar musu da wiwi

Uruguay ta zama kasa ta farko a duniya da ke nomawa da sayar da tabar wiwi a dokance don nishadi.

Tun da farkon safiyar Laraba ne mutane suka kafa layuka a gaban kantunan sayar da magunguna guda 16 da ke da izinin sayar da wiwi. Kuma da tsakar rana ne tabar ta kare a akalla daya daga ciki kantunan.

Don hana wiwin shiga hannun masu yawon shakatawa, 'yan kasar Uruaguay ne kadai da suka haura shekara 18 ka iya yin rijista don saye.

Ta hanyar amfani da shaidar zanen yatsu, mutum na iya sayen sama da gram 40 duk wata don yin bushi.

Ana sayar da nau'i biyu na tabar ta wiwi, duka na kunshe da sinadarin THC (tetrahydrocannabinol) wani kwakkwaran mahadi da ke sa kai ya yi caji.

Manufar wannan sauyi ita ce rage fataucin tabar.

Masu aikowa BBC rahotanni sun ce kasashen Latin Amurka na kara neman hanyar musanya haramcin tabar wiwi da wasu tsare-tsare.

Labarai masu alaka