'Ya kamata a yi bayani kan matan da Boko Haram ta sace'

Boko Haram Hakkin mallakar hoto .
Image caption Kungiyar Boko Haram ta sha garkuwa da mutane

A Najeriya masu sharhi kan al'amuran yau da kullum sun ce ya kamata hukumomi su fito su bayyana gaskiyar al'amarin batun sace 'yan sanda mata da mayakan Boko Haram suka yi.

Sun dai sace su ne a ranar 20 ga watan Yuni, lokacin da suke hanyar zuwa jana'izar daya daga cikin su a hanyar Damboa da ke jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.

Jafar Jafar wani mai sharhi kan al'amuran yau da kullum na ganin ya kamata gwamnati ta yi bayani, saboda irin hakan ce ta faru da gwamnatin da ta gabata a lokacin da aka sace 'yan matan sakandaren Chibok a lokacin da suke zana jarrabawa.

Ya kuma ce wani abu da zai bayar da mamaki shi ne, a kasashen ketare ko da mutum daya aka sace sai hankula su tashi a bazama nema har sai an kai gaci, amma a Najeriya sai a yi ta kumbiya-kumbiya.

''Ya kamata gwamnati da jami'an tsaro su rika yin gaggawar bayyana abin da ya faru ga 'yan uwan mutanen da aka sace, ba wai lallai sai sojoji ko 'yan sanda ba alhakin kula da 'yan Najeriya ya rataya a wuyansu, don haka ban ga dalilin da zai sa a yi ta kwan-gaba kwan-baya a kan batu guda ba.''

A ranar Litinin ne kungiyar Boko Haram ta fitar da wani faifan bidiyon da ya nuna wasu mata da motar 'yan sanda da suka yi ikirarin garkuwa da su duk da a baya, Rundunar 'yan sandan Najeriyar na cewa a iya saninsu, ba a yi garkuwa da wasu jami'ansu ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Babban hafsan sojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai ya ce za su yi bakin kokarinsu wajen shawo kan matsalar Boko Haram

Haka kuma a hirar da BBC ta yi da babban hafsan sojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai ya sake nanata cewa jami'an 'yan sanda sun tabbatar da ba ma'aikatansu ba ne amma ana gudanar da bincike don gano bakin zaren da kubutar da matan.

Dangin matan dai, sun nemi hukumomin Najeriya su agaza wajen kubutar da su.

Daya daga cikin 'yan uwan wadannan mata su takwas ya ce duk da yake hankalinsu ya kwanta da su ka ga shaidar cewa suna raye, amma abin da zai fi faranta masu rai shi ne su ga an dawo da su gida.

Mayakan Boko Haram dai sun sha sace mata da maza, da kananan yara a Najeriya musamman a yankin arewa maso gabashin kasar, inda sojojin kasar suka yi nasarar kubutar da wasu ciki har da wasu daga cikin 'yan makarantar sakandaren Chibok da aka yi garkuwa da su.

A bangare guda kuma mayakan na ci gaba da kaddamar da hare-hare a yankunan jihar Borno, na baya-bayan nan da suka zafafa kai wa dai ya hada da jami'ar Maiduguri.

Labarai masu alaka