Nigeria: Rashin tsaro da hanyoyi na hana aikin riga-kafi

Alurar rigakafi
Image caption Allurar rigakafi ko digon baki na bai wa jarirai da yara kariya daga kamuwa da cututtuka kamar, kyanda, zazzabin cizon sauro, da polio ko shan inna

Wani sabon rahoto da hukumar lafiya da asusun yara na UNICEF suka fitar, ya ce a cikin jarirai goma da ke duniya, ba a yi wa daya allurar rigakafi ba a bara a wasu kasashe ciki har da Nijeriya.

Ya kuma ce haka zai iya jefa rayuwarsu cikin hadarin kamuwa da cututtukan da za a iya hana abkuwarsu.

Rahoton ya ce tun a shekarar 2010 ne tsarin allurar rigakafin ya fuskanci tsaiko.

Ya kuma yi nazari ne kan tsarin allurar rigakafi a kasashe 194 na duniya, ciki har da Najeriya.

Dr Betta Edu ita ce darakta janar da hukumar kiwon lafiya matakin farko a jihar Cross River a kudancin Najeriyar, ta shaidawa BBC cewa gwamnatin daga matakin tarayya har zuwa jihohi na bakin kokarin su wajen tabbatar da cewa an yi wa jarirai da kananan yara allurar riga-kafi ko digon baki.

Sai dai ta ce ana samun matsalar isa wasu wuraren a sassan kasar, dalili kenan jami'an lafiya ba sa iya zuwa wadannan yankunan.

Akwai kuma batun kalubalen da bangaren kiwon lafiya ke fuskanta, allurar riga-kafi daya ce daga saukakan hanyoyin magance matsalolin cututtukan da ke saurin kama jarirai ko yara kanana.

Rashin kyawun hanyar da za a iya shiga yankunan karkara,da wasu wuraren da ke fama da yaki, ko wuraren da koguna suka kewaye, ku kuma tsaunuka da yankunan da mota bata isa wurin na daga cikin manyan matsalolin da ke kawo tsaikon aikin rigakafin.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Akwai kalubale sosai wajen aikin riga-kafi a Nijeriya

Dr Betta ta kara da cewa ''Mun damu matuka, wannan dalili ne ma muka ce a duk lokacin da ka iya ganin yaran da suka kamu da irin cututtukan ko da ma ba su kamu da ita ba a yi gaggawar taimaka don yi musu riga kafi.''

Ta kuma ce yanzu an fara gano bakin zaren ta hanyar daukar wasu matakai da suka hada da sake yi wa hukumar kiwon lafiya matakin farko garanbawul.

Dr Betta ta kara da cewa a halin da ake ciki ma za su je iyakar Najeriya da jamhuriyar kamaru, a yankin Bakassi , don tattaunawa kan yadda za a gudanar da aikin.

''Su ma ma'aikatan sakai a yankuna sun fara samun horo dan taimaka mana gudanar da aikin, ina ganin indai komai ya tafi daidai ba mu da wata matsala''. Inji Dr Betta.

Babu wata kididdiga a hukumance da za ta tabbatar da yawan yaran da ba a yi wa allurar rigakafi ba a shekarar da ta gaba, amma Dr Betta ta ce adadin bai kai kashi 80 cikin 100 ba.

Labarai masu alaka