Dan Masar ne ya ci gasar kirkira ta Afirka

Ali El Shafei daga kasar Masar ne ya yi nasara a gasar ta bana
Image caption Wannan shi ne karo na shida da ake yin gasar kirkire-kirkire ta Afirka

A kasar Ghana an gudanar da taron bayar da lambar yabo ta kirkire- kirkire a nahiyar Afirka na wannan shekarar da aka yi a birnin Accra na kasar.

Matasa goma ne dai aka zabo daga nahiyar Aiurka, dan shiga wannan gasa ciki kuwa har da Najeriya.

Taron na bana shi ne karo na shida da ake yi da nufin zaburar da matasa da basu kwarin gwiwar kirkiro abubuwan da al'uma za su amfana da shi.

Dakta Olawale Olanisolu dan Najeriya ne, kuma likitan kirji, da ya kirkiro wata na'urar gwaji dan gano cutar tarin fuka cikin minti 10, ba a bukatar daukar jini ko fitsari ya yin gwajin, gumin jikin dan adam shi ake amfani da shi dan tantancewa.

Sai dai kuma wani dan kasar Masar ne mai shekara 58 farfesa Aly El Shafei ne ya yi nasarar lashe gasar ta bana da, wanda malami ne a jami'ar birnin Alkhahira.

Shi ya yi nasarar lashe kyautar dala 100,000 yayin da wanda ya yi na biyu kuma zai dauki dala 25,000, sannan kuma akwai lambar yabo ta musamman ga wanda ya kirkiro abinda ya yi tasiri sosai a kan al`umma.

Shi ma za a bashi dala 25,000, sannan kuma sauran mutane bakwai da ke cikin gasar, ko wanne zai samu dala dubu biyar-biyar, sannan kuma daga baya, akwai wani shirin samar musu tallafin ci gaba da ayyukansu.

Labarai masu alaka