Yaron da aka dasawa hannu ya fara buga kwallon gora

Likitoci 40 ne suka taka rawa a dashen hannun da aka yi wa yaron, wanda shi ne karon farko da aka fara yi a duniya
Image caption Zion ya ce a lokacin da ya ke shekara biyu a duniya, dole aka yanke masa hannaye saboda ba shi da lafiya

Yaro na farko da aka fara kafa tarihi a duniya, da kuma aka yi wa dashen hannu ya fara yin wasan kwallon gora da hannun kamar yadda likitansa ya bayyana.

Shekara biyu kenan da aka yi wa Zon Harvey aikin da aka dasa masa hannun, likitocin da ke kula da yaron sun ce sun yi mamakin yadda lokaci kalilan hannun ya saje da jikinsa.

Zion mai shekara 10, ya samu ci gaban ne bayan dashen hannun da kwararrun likitoci suka yi masa, a halin da ake ciki yana iya cin abinci, har ma da yin rubutu.

Likitocin sun ce duk da cewa hannun da aka dasa masa wani ne ya ba shi kyautarsa, amma kwakwalwarsa ta karbi sabon bakon al'amarin da ya zo mata katsahan.

Daya daga cikin likitocin da suka yi wa Zion aiki a asibitin yara na Philadelphia wato Dakta Sandara Amaral, ta shaidawa BBC cewa a ko da yaushe ana samun ci gaba kan yadda yaron ke amfani da hannun tamkar tun ainahi nasa ne.

Ta kara da cewa abin mamakin shi ne yadda Zion ke rubuta sunansa da wasu kalmomi cikin sauri, ya kuma kamo fuskar mahaifiyarsa da hannun tare da sumbatar kumatunta ba kamar farkon aikin da ba ya ma iya motsa hannun ba.

Kungiyar likitocin da suka yi wa Zion aiki, sun wallafa dukkan bayanan yadda aka yi wa yaron aiki tun daga farko har karshe, da ci gaban da aka samu a wata mujallar Lancent, a shafin da ke bayani a kan yara wato Child and Adolescesnt Health jounal.

Labarai masu alaka