Iran na taimaka wa kungiyar Hezbollah - Amurka

Hassan Rouhani Hakkin mallakar hoto Ebrahim Noroozi
Image caption Iran ta sha musanta alakarta da ta'addanci

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce Iran ce take tallafawa ta'addanci da kudadenta, a duniya.

Ma'aikatar ta yi la'akari ne da irin tallafin da kasar ta Iran take bai wa kungiyar Hezbollah.

Ma fi yawancin 'ya'yan kungiyar Hezbollah dai mabiya mazhabar Shi'a ne.

'Yan kungiyar ta Hezbollah dai na ikrarin fafutukar kare kai daga mutanen da suke kira makiyan musulunci.

Hezbollah ta yi suna wajen kai hare-hare kan Yahudawa, al'amarin da ya tsaya wa kasar Isra'ila a rai.

A rahoton Amurkar na 2016, ma'aikatar harkokin wajen ta bayyana kungiyoyi irin su IS da Alqaeda da Taliban da wadanda suka yi fice wajen ayyukan ta'addanci.

Sai dai kuma rahoton bai nuna kasar Iran din na da alaka da wadannan kungiyoyin ba.

Har wa yau, rahoton ya ce yawan mace-mace sakamakon hare-haren ta'addanci sun ragu a 2016 a kasashen duniya.