Bincike kan kutsen Rasha a zaben Amurka ya zafafa

Donald Trump
Bayanan hoto,

Tun bayan zaben da aka gudanar, ake cece-kuce kan yiwuwar Rasha ta yi kutse a zaben na Amurka da ya bai wa Mista Trump damar zama shugaban kasa

Kafafen watsa labaran Amurka sun ce mai magana da yawun tawagar lauyoyin Shugaba Donald Trump ya yi murabus.

Mark Corallo dai ya dade yana magana da yawun lauyoyi masu kare shugaban na Amurka a binciken da ake yi kan alakar Mista Trump da kasar Rasha.

Rahotanni sun ce lauyoyin suna sanya ido kan mutanen da ke jagorancin binciken alakar Mista Trump da Rashar.

Jaridar New York Times ta ce lauyoyin na Mista Trump suna kokarin gano miki a tattare da masu binciken da manufar kunyata su, to sai dai shi Mista Corallo bai amince da daukar irin wannan matakin ba.

Binciken, wanda Mai Bincike na Musamman Robert Mueller ya ke jagoranta, ya fadada tare da samar da karin bayanai a 'yan makwannin da suka wuce.

An kara samun cigaba a aikin da Mista Mueller ke jagoranta, don a halin da ake ci an kara samun wani bayanin kan cewa akwai hannun masu kula da shige da ficen kudaden Shugaba Trump da su ma ake bincikarsu.

Kawo yanzu Mark Corallo bai sanar da dalilin yin murabus din ba, sai dai masu sharhi sun yi hasashen ta yiwu lamarin na da nasaba da dambarwar kutsen na Rasha.