Cutar amai da gudawa ta barke a Yemen

Yara da yakin Yemen ya shafa
Bayanan hoto,

Rashin tsaftataccen ruwan sa da muhalli da samun magani na daga cikin matsalolin da al'umar Yemen ke fuskanta

Kungiyar bayar da agaji ta Oxfam ta yi gargadin cewa mutanen da suka kamu da cutar amai da gudawa a kasar Yemen na fa cigaba da karuwa.

Fiye da mutane 360 ne dai a ka yi hakikance sun kamu da cutar, a barkewar da ta yi mafi muni tun bayan fara yakin da kasar ke ciki, kuma tuni mutane 1800 sun mutu.

Yakin da ake gwabzawa wanda Saudiya ke goyon baya, ya janyo rashin samun tsaftataccen ruwan sha da tsaftar muhalli, da rashin magunguna ga wadanda suka kamu da cutar.

Ba wannan ne karon farko da cutar amai da gudawar ke barkewa a kasar Yemen ba, sai dai wannan karon ne cutar ta yi kamari da yaduwa cikin kankanin lokaci.

Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin yara na cikin mawuyacin hali, babu abinci mai gina jiki, babu ruwan sha ko magani da muhalli mai tsafta.

Haka kuma kusan cikin kowanne minti 10 yaro daya ne ke mutuwa a kasar ta Yemen, sanadin kamuwa da cutattukan da za a iya magance su kamar dai amai da gudawar amma rashin samun damar isa wurin da mutanen ke fakewa ya ke haddasa mutuwarsu.

Bangaren kiwon lafiya a kasar na gab da durkushewa, fiye da mutane miliyan 19 ne ke zama babu ruwan sha, ya yin da wasu miliyan 14 ke tsananin bukatar taimakon abinci da magani kuma lamarin ya fi shafar yara.