Daliban Kudancin Kaduna sun kai karar gwamnatin jihar

Asalin hoton, Kaduna Government
Jami'ai dai sun musanta zargin cewa gwamnatin na son sauya wa makarantun mazauni ne.
Kungiyar matasa da dalibai ta yankin Kudancin jihar Kaduna ta Najeriya ta koka kan rashin bude wasu manyan makarantunsu 3 da gwamnatin jihar ta rufe a karshen shekarar data gabata.
Yanzu haka dai Kungiyar ta kai kara ga hukumar kare hakkin bil'adama da kuma Majalisar dokokin kasar don neman a tursasawa gwamnatin jihar ta bude makarantun.
A watan Disamba bara ne gwamnati ta rufe reshen jami'ar jihar da ke Kafanchan da Kwaleji Nazari Aikin Malanta da ke Gidanwaya da Kuma wata kwalejin koyon aikin ungozoma bayan wani rikici a yankin da haddasa salwantar rayukka da dukiyoyi; har sai tsaro ya inganta.
Sai dai da yake zantawa da BBC bayan gabatar da koken nasu a birnin Abuja ranar Litinin, Shugaban kungiyar Comrade Galadima Jesse ya ce gwamnatin ba ta da dalilin kin bude makarantun domin yanzu tsaron ya inganta.
''Ba wani takaimaimen dalili cewa kan tsaro ne aka rufe makarantun nan; idan ka duba akwai kananan makarantu na firamare da sakandare suna nan suna tafiyar da lamurransu. Idan har saboda tsaro ne to bai kamata a bar yara kanana suna ci gaba da zuwa makaranta ba.''
Amma gwamnatin ta nace kan cewar fargabar kan rashin tsaron ce ta sa makarantun ke ci gaba da zama a rufe.
''Majalisar tsaro ta jiha ce ke da hakkin cewa yanzu tsaro ya inganta; to in sun ba da shawarar cewa a kara ba da lokaci ai dole a dan kara hankuri,'' inji Kwamishinan Ilimi na jahar Farfesa Andrew Nok.