Pakistan: An yi wa wata fyaden ramuwar gayya

Pakistan

Asalin hoton, AFP/Getty Image

Bayanan hoto,

Wani mutumin yankin yana nuna gidan da aka yiwa matashiyar fyade a kauyen Muzaffarabad, na garin Multan

'Yan sanda a Pakistan sun cafke mutum 20 a garin Multan, kan bayar da umarnin a yi wa wata matashiya fyade, a matsayin ramuwar gayya kan zargin da ake yi wa dan uwanta na aikata fyaden.

Yan sanda sun ce iyalan 'yan matan biyu suna da dangantaka, kuma duka bangarorin biyu ne suka hada kai wajen yanke shawarar abin da ya kamata a yi.

" Wata kungiyar dattawan kauye ce da ake yi wa lakabi da Jirga ta bayar da umarnin da a yi wa budurwar mai shekaru 16 fyaden a matsayin ramuwar gayya,'' jami'in dansanda Baksh ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Ya ce wani mutum ne ya kai kara wurin majalisar hukumar kauyen cewa an yi wa kanwarsa mai shekara 12 fyade.

Hukmar sai ta bai wa mai kai karar umarnin shi ma ya je ya yiwa kanwar wanda ake zargin fyade a matsayin ramuwar gayya- wanda 'yansanda suka ce sai ya aikata.

Jaridar 'Dawn' ta kasar Pakistan ta bayar da rahoton cewa an tliastawa yarinyar bayyana a gaban taron jama'a har da iyayenta, inda aka yi mata fyaden.

Daga bisani uwayen 'yan matan biyu sun gabatar da kara a caji ofis na 'yansanda.

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Bayanan hoto,

Wani daki a kauyen Muzaffarabad a Pakistani inda aka bayyana an yiwa matashiyar fyade

Binciken da likitoci suka yi ya tabbatar da cewa duka 'yan matan an yi musu fyade.

Wani jami'in 'yansanda Ahsan Younas, ya shaida wa BBC cewa yarinyar ta farko da aka yi wa fyaden za ta kai tsakanin shekara 12 zuwa 14, yayin ta biyun wacce aka yi ramuwar gayyar a kan ta za ta kai tsakanin shekara 16 zuwa 17.

Ya kuma ce 'yansanda sun yi rajistar koke-koke kan mutane 25, kana wanda ake zargi da yi wa 'yar shekara 12 fyade ya gudu.

Kungiyar dattawan da ake wa lakabi da Jirga, ana kafa ta ne don shawo kan matsaloli ko rikici a kauyukan kasar Pakistan.

Amma kuma hukumomi na daukar irin wannan kungiya a matsayin haramtacciya---wacce ta sha yanke hukunce-hukunce masu cike da takaddama.

Asalin hoton, BHASKER SOLANKI/BBC

Bayanan hoto,

Mukhtar Mai, a shekara ta 2011, da aka yi wa fyaden taron dangi a bisa umarnin kungiyar dattawan yankinsu

Ko a shekara ta 2002 wannan kungiya ta Jirga ta taba bayar da umarni a yi wa wata mata mai suna Mai Mukhtar mai shekara 28 fyaden taron dangi, bayan da aka zargi kanenta mai shekara 12 da yin mu'amala da matar da da girme shi.

Ms Mai ta kai karar wanda ya yi mata fyaden gaban kuliya - matakin da ba kowa ke da karfin gwiwa dauka ba saboda fargabar nuna kyama.