Boko Haram ta kashe sojojin Nigeria tara a Borno

Wasu Sojojin Najeriya

Asalin hoton, Nigeria Army

Bayanan hoto,

An dai kai gawwakin sojojin tare da wadanda suka raunata zuwa wani asibiti a Maiduguri

Rundunar sojan Najeriya ta ce kawo yanzu sojojinta 9 sun mutu tare da wani farar hulla daya a garin kubutar da wani ayarin masana masu bincike da mayakan Boko Haram suka kama a cikin wani kwanton bauna a jihar Borno.

Sai dai ta ce sun yi nasarar kubutar da yawancin mutanen, ko da yake sai nan gaba ne za ta fitar da cikakken bayani a kan batun.

A ranar Talata ne 'yan Boko Haram suka yi wa mutanen da suka hada da malaman jami'ar Maiduguri kwanton bauna a kauyen Jibi a jihar Borno.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar sojan kasar Brigadiya-Janar Sani Usman Kukasheka ya fitar ranar Laraba da dare, sojojin sun ce duk da wannan hasarar da suka yi, kokarin binciken inda sauran wadanda ake garkuwa da sun na ci gaba da zimmar kubutar da su.

Sanarwar ta ce sojojin sun kuma kashe tare da raunata adadi mai yawa na mayakan kungiyar Boko Haram da ake zargi da sace mutanen.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Daga cikin sojojin 9 da suka kwanta-dama akwai wani mai mukamin leftanant.

Haka ma sojojin sun ce sun kwato motoci guda hudu da suka hada da motoci 2 kirar hilux da suka masu garkuwar kwace daga ma'aikatan kamfanin na NNPC da wata daya ta mayakan sa-kai na Civilian JTF.

Sai dai sanarwar bata bayyana ko mutane nawa sojojin suka kubutar ba daga cikin masu binciken kawo yanzu da kuma ko nawa ake nema.

Masana kimiyyar albarkatun kasa goma ne daga Jami'ar Maiduguri kamfanin man na NNPC ya bai wa aikin wani bincike kan danyen mai a yankin dake daura da tafkin Chadi kuma kafin sanarwar sojojin ya tabbatar cewa an kubutar da uku daga cikinsu.

Sai dai Wani ganau ya shaida wa BBC cewa an kashe da dama daga cikin masu binciken da wadanda ke yi musu rakiya kuma akwai wasu da har yanzu ba a san inda suke ba.

Wasu majiyoyin kuma sun ce daga cikin sojojin da aka kashe a cikin arangamar kubutar da su dai har da wani mai mukamin leftenant.