Amurka ta saka wa jami'an Venezuela 13 takunkumi

Asalin hoton, AFP
Ana zargi Mr. Maduro dan son yin mulkin kama-karya.
Shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro ya yi fatali da takunkumin da kasar Amurka ta kakaba wasu manyan 'yan siyasa da jami'an sojin kasarsa goma sha uku.
Amurka dai ta ce ta dauki matakin domin nuna wa Mr. Maduro cewa da gaske take a barazanar ta yi na kakaba wa Venezuela takunkumi karya tattalin arziki cikin sauri idan ya ci gaba da shirinsa na gudanar da wata kuri'ar da aka shirya yi ranar Lahadi mai zuwa domin kafa wata sabuwar majalisar dokoki.
Wadanda aka kakabawa takunkumin dai sun hada da shugabannin rundunonin soji da 'yansandan kasar da daraktar hukumar zabe ta kasa, da da kuma mataimakin shugaban kamfanin mai na kasar kazalika da wani tsohon mataimakin shugaban kasar bisa zarginsu da hannu dumu-dumu wajen tafka almundaha da kuma keta hakkin bil'adama.
Kasar ta Amurka haka kuma ta bukaci shugaban na Venezuela da ya yi watsi da shirinsa da gudanar wani zaben 'yan majalisar dokoki masu ikon sake rubuta kundin tsarin mulki; da ke jawo takaddama a kasar.
Takunkumin dai ya zo ne rana guda da soma wani yajin aikin gama-gari na kwanakki biyu da 'yan adawa suka kira domin kara hurawa shugaban wuta ya soke shirin zaben sabbin 'yan majalisar.
Asalin hoton, JUAN BARRETO
Mutum daya ya rasa ransa a ranar farko ta yajin aiki.
Madugun 'yan hamayyar Leopoldo Lopez wanda yanzu ake yi wa daurin talala a gidansa; ya yi magana da magoya bayansa ta wani faifan bidiyo.
''Ina son fada wa daukacin 'yan Venezueala cewa wannan fadan ya soma ne a kan tituna, kuma haka ya kasance a kan tituna kuma zai ci gaba da gudana kan tituna. Dole mu ci gaba da shi har sai mun samu 'yanci, da wanzuwar dimokradiyya da kuma zama lafiya ga dukkanin 'yan Venezuela''
Sai dai Shugaba Maduro ya lashi takobin gudanar da zaben na ranar Lahadi domin zabar sabuwar majalisar mai ikon sake rubuta kundin tsarin mulki kuma ta maye gurbin wadda ake da ita yanzu da ke karkashin jagorancin 'yan adawa.
Ya ce yin hakan ne zai kawo zaman lafiya bayan kwashe watanni hudu ana zanga-zangar kin jinin gwamnati wadda ta yi sanadin mutuwar mutane fiye da dari daya.