Nigeria: Me ya sa matasa ba sa sha'awar zaben kansu a mukamai?

Matasa ke zanga-zanga a Abuja
Bayanan hoto,

Matasa na zanga-zangar lumana a Abuja, kan damar yin takarar mukamai a shugabancin Najeriya

A kan ce mata su ne makiyan mata 'yan uwansu, amma kuma sai ga shi matasa a Najeriya ma na bin sahu, inda ga dukkan alamu ba su bayar da cikakken goyon bayan su ga masu neman takarar shugabancin kasar.

A ranar Talata ne 25 ga watan Yuli 2017 ne gamayyar wasu kungiyoyin matasa fiye da 50 suka yi tattaki zuwa zauren Majalisar dokokin Najeriya, domin nuna rashin amincewa da yunkurin da ake zargin 'yan Majalisar suna yi, na janye wani kuduri da zai rage shekarun da mutum zai iya yin takarar mukaman siyasa.

Matasan sun ce sun yi zanga-zangar lumana ne domin matsawa majalisar lamba su bar kudurin, wanda ake ganin zai bai wa matasa damar shiga a dama da su a harkokin shugabancin kasar.

Hakazalika sun ta tafka muhara a shafukan sada zumunta kan maudu'in #NotTooYoungToRun.

Bayan haka ne Majalisar dattawan Najeriya, a ranar Laraba 26 ga watan Yulin 2017, ta amince da kudirin da zai bai wa matasan damar takarara mukaman shugaban kasa da gwamna da dan majalisar dattawa da na wakilai.

Kudirin dai ya bai wa matasa masu shekara 35 damar shiga takarar neman shugabancin kasar yayin da ya bai wa matasa masu shekara 30 damar neman gwamna.

Hakazalika, kudurin ya amince 'yan shekara 25 su tsaya takarar zama wakilai a majalisar wakilan kasar.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Duk da wannan nasarar da matasan Najeriya suka samu, akwai masu kokwanto da kamun ludayin matasa a shugabancin.

Wani lamari ba wai a Najeriya ne kadai ba, har da kasashen yamma ma, misali Amurka, inda a yayin yakin shugabancin kasar, Matasa suka bayar da goyon bayan su sosai ga Bernie Sanders, wani tsohon da siyasar kasar.

Amma kuma idan aka yi waiwaye adon tafiya, wadanda suka kafa gwamnatin Najeriya tun farko ma matasa ne, daga kan Primiya Sir Tafawa Balewa wanda ya yi Firayi Minista a kasa da shekara 50, da Sir Obafemi Awolowo wanda a shekara 45 ya yi Primiyar yankin kudu yammacin Najeriya, haka shi ma Ahmadu Bello Sardaunar Sakwatto, wanda ya yi Primiyar yankin arewa a kasa da shekara hamsin, dai dai sauransu.

Tsohon shugaba Yakubu Gowon, wanda shi ne shugaba mafi kankantar shekaru da aka taba yi, inda a shekara 32 kacal ya shugabanci Najeriya.

To ko menene ya sa a yanzu matasa ba su da kwarin gwiwar yin takara?

Ahmed Buhari, wani matashi ne da a yanzu ke neman yin takarar shugabancin Najeriya nan da shekarar 2019, ya bayar da nasa dalilin da ya sa matasa ke zillimin zaben 'yanuwansu matasa.

Asalin hoton, Ahmed Buhari Facebook

Bayanan hoto,

Wani matashi da ke goyon bayan 'yanuwan sa su yi takarar mukamai

"Yanzu matsalar matasa ba sa siyasa in ba da kudi ba, duk inda kudi yake nan suke, duk da cewa yanzu a yayin gudanar da kamfe din mu, mun gano cewa, yanzu ma matasan idanun su ya bude, saboda ko sun amshi kudi ma idan Allah Ya kawo lokacin zabe, ba sa kada kuri'arsu ga wanda ya basu."

Game da ko matasan ba sa tunanin wani cikin su na da kwarewar shugabanci, Ahmad Buhari ya ce,

"Ba komai ba ne sai don sun saba da ganin tsoffi a mulki, matasan sun kuma dade suna zaune kawai, ba tare da nuna kishin neman wani mukami ba, don haka matasa suke ganin babu abun da zasu iya musu,"

"Baya ga haka kuma matasan namu na yanzu sun taso tun suna 'yan shekaru kalilan wadanda ke mulki a wannan lokaci, su ne har yanzu rike da kasar." In ji Ahmed Buhari

Ahmed ya kammala da cewa matasa na bukata su san cewa goyon nasu na da fa'ida, kuma su daure su daina sanya son zuci a lamuran da ya shafi siyasa, sai dai cigaban kasa da al'ummarsu.

Ga alama dai wannan zanga-zangar lumana da matasa suka yi ya yi tasiri, ganin yadda a yanzu Majalisa ta amince da kudirin dokar da za ta ba matasa damar takarar mukamai.

Amma kuma ba nan gizo ke sakar ba, tunda ana bukata matasan su nuna kwazo wajen ganin wani nasu ya hau mukami, domin su nuna kwarewarsu wajen tafiyar da mulki.

Bayanan hoto,

Sakwannin shafin BBC Hausa Facebook inda ake tafka muhawara kan wanna batu

Kamar yadda a cewar Muhammad Asheeru Babaji, wani ma'abocin BBC na shafin Facebook, wanda shi a ra'ayin sa ya ce,

"Ni matashine amma bana goyon bayan a ba wa matashi wannan dama, ta a rage shekaru, domin tsayawa takara, hujja -- Matasa yawancin su basu mallaki hankalin kan su ba, misali, matasa a kasarinsu manema matane, da shaye-shaye, su ne sata, su ne harkar da duk bashi da amfani, za ka ga matasa ne, sh iyasa wadanda suka kawo tsarin mulkin duniya, suka tsara dattawa su adda mulki, saboda ana tunani in mutum ya manyanta ba za a same su da hayaniya ba."

Dr Usman Isyaku, kuma wani mai sharhi kan siyasa a Najeriya, ya ce a ganin sa, dalilin da ya sa matasa ba sa goyon bayan 'yanuwansu, shi ne saboda rashin kudi, suna ganin sai masu kudi ne ke takara.

A cewar Dokta Usman, babu hadin kai tsakanin matasa, musamman saboda an samu rabuwar kawuna ta fannin kabilanci da addini da bangaranci, a yayin da masu shekaru da ke takara a siyasa su ke da basirar hada kansu har su kafa jam'iyyar siyasa mai dorewa.

A ra'ayin Usman Gurama kuma, wani matashi mai sharhi kan harkokin yau da kullum a shafukan sada zumunta, dalilin da ya sa matasa ba sa samun amincewa al'umma wajen shugabanci, shi ne saboda rashin kudi.

Asalin hoton, Usman Gurama Facebook

Bayanan hoto,

Usman Gurama ya ce matasan Najeriya damban su ke da na sauran kasashe

Manyan a cewarsa, ba su sakan masu mara ba, sun riga sun dandana mulki, don haka ba sa son su saki, haka kuma ba sa sakin kudin da zai bai wa matasan damar yin takarar.

Duk da haka, Gurama ba ya goyon bayan matasa su yi shugabanci, duk da cewa shi kan sa matashi ne, ga kuma dalilansa,

"Matasan Najeriya damban su ke da na sauran kasashe," in ji Gurama.

Ya kara da cewa, "Yawanci suna kosawa su gama karatu ne domin su yi kudi, ba wai saboda kasa ta karu da su ba, ko wata akida ta su mai inganci."

Masu fashin baki dai sun jaddada cewa, mafi yawan al'ummar Najeriya, na da tunanin cewa abin da babba ya hango, yaro ko ya hau tsauni ba zai hango shi ba, don haka ake wa matasa kallon ba su nisan tunanin daukar shawara game da mulki.

Najeriya dai na sauraro su ga gudun ruwan shugaban su da suka zaba, watau Muhammadu Buhari, wanda ya hau mulki yana da shekaru 72, kuma an zabe shi ne bisa bukatar ganin canji a kasar.

Canji kuma na iya daukar kamanni iri-iri, ciki har da zaben matashi da zai jagoranci al'ummar kasar, kamar yadda shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya yi nasarar samu yardar al'ummar kasarsa a shekara 39.