Ana gano shirin aringizon sakamakon jarabawa a Ghana

Wani ajin koyon Faransanci a Ghana
Image caption Hukumar ta gargadi daliban da su yi taka-tsantsan da 'mayaudara.'

Hukumar Shirya Jarrabawa ta Yammacin Afrika (WAEC), ta ce ta bankado wani yunkuri da wasu mutane ke yi wa wasu daliban da suka zauna jarabawar kammala sakandare a kasar Ghana gyaran sakamakonsu kafin a fitar da shi.

A cikin wata hira da BBC, Shugabar Sashen Hulda da Jama'a na hukumar a kasar Madam Agnes Kujo, ta ce hukumar ta gano wasu ''bata-gari'' wadanda ke cewa suna da kafar shiga rumbun adana bayanai na hukumar, na yi wa wasu dalibai alkawalin sauya musu sakamakon jarabawarsu.

''Mun gargadi dalibai dangane da wasu bata-gari da ke musu alkawalin inganta musu sakamakon jarabawarsu idan suka bayar da kudi.'' In ji ta.

Madam Kujo ta ce kuma tuni wasu daliban suka biya kudaden amma daga bisani ba su samu biyan bukata ba; saboda a cewarta mutanen 'yan damfara ne kawai.

Ta kara da cewa da cewa rumbum ajiye bayanan sakamakon jarrabawar ta WAEC na da cikkaken tsaro, kuma za a iya gano duk wanda yake da sakamakon boge.

Wakilin BBC a kasar ta Ghana ya ce sai dai tuni hukumar ta yi maza ta wallafa sakamakon a shafinta na intanet ta yadda dalibai za su yi dubawa.

''Jimillar dalibai dubu 289 da 210 ne suka rubuta jarrabawar WAEC a wannan shekara, adadin da ya haura adadin daliban da suka rubuta jarabawar a bara da kashi 4.5%.'' In ji wakilin namu Muhammad Fahad Adam.

Labarai masu alaka