Juyin Mulki: Turkiyya za ta soma yi wa mutum 500 shari'a

Shugaban Turkiyya Racep Erdogan Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shugaban Erdogan dai ya farke layar juyin mulkin ne ta amfani da Twitter.

Nan da dan lokaci ne ake soma wata muhimmiyar shari'a a kasar Turkiyya inda za a gurfanar kusan mutane 500 a gaban kotu bisa zarginsu da hannu a shirya juyin mulkin da bai yi nasara ba a bara.

Babban wanda ake tuhuma shi ne malamin addinin musuluncin nan da ke zaune a Amurka Fathullah Gullen wanda gwamnati ke zargi da kitsa juyin mulkin; kodayake ya musanta.

Zaman kotun na ranar Talata dai zai mai da hankali ne kan abubuwan da suka faru a sansanin mayakan saman kasar na Akinci da ke birnin Ankara.

''Daga sansanin ne dai jirgin da ya jefa bama-bamai kan ginin majalisar dokoki ya tashi kuma anan ne aka tsare babban hafsan soja da wasu manyan kwamandoji,'' in ji wakilin BBC a birnin na Ankara.

Gwamnati dai ta yi imanin cewa daga sansanin ne aka jagoranci yunkurin juyin mulkin na bara.

Wadanda ake tuhuma 486 ne za a gurfanar gaban kotun a wannan shari'a amma bakwai daga cikin mutanen da ake zargin ba su shiga hannu ba; cikinsu har da babban wanda ake tuhuma wato Fathullah Gullen da kuma da daya daga cikin wadanda ake jin su ne suka jagorancin yunkurin wato tsohon babban hafsan sojan sama Adil Oksuz.

Ana zargin wadanda ake tuhumar da aikata laifukka kamar keta tsarin mulkin kasar, da yunkurin kashe shugaban kasa, da yunkurin kifar da gwamnatin turkiyya da kuma shugabantar kungiyar 'yan ta'adda.

Fiye da mutane 40 daga cikinsu za su fuskanci daurin rai-da-rai maras sassauci idan aka same su da laifi.