'Akwai yiwuwar kwalara ta kashe yara miliyan 1 a Yemen'

Wani yaro mai fama da tamowa a Yemen Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yanzu dai yawan masu kamuwa da cutar a kasar ya kai 430,000.

Kungiyar tallafawa kananan yara ta Save The Children ta ce yara miliyan daya na cikin babbar kasadar mutuwa sakamakon cutar kwalara a kasar Yemen.

Ta ce sun shiga cikin wannan halin ne saboda yadda suke fama da matsanancin karancin abinci kuma suna zaune ne a yankunan da kasar da lamari ya fi muni.

A cewar Save The Children, yaran da ke da tamowa sun fi zama cikin kasadar mutuwa ninkin-ba-ninkin idan suka kamu da kwalara, fiye da wadanda ba su da ita; saboda garkuwar jikinsu ta yi rauni ta yadda ba ta iya fada da kwayoyin cutar da ake dauka daga gurbataccen ruwa.

Daga cikin yaran 'yan kasa da shekara biyar, miliyan daya da ke da matsananciyar tamowa kuma ke rayuwa a yankunan da cutar ta fi kamari, kungiyar ta ce dubu 200 na cikin kasadar mutuwa nan take saboda yunwa.

''Fiye da mutane 1900 ne suka mutu sakamakon cutar a kasar ta Yemen daga watan Afrilu zuwa yau, sulusinsu 'yan kasa ga shekaru 15,'' in ji wakiliyar BBC kan harkokin lafiya.

Cutar Kwalara dai ba ta da wuyar magani, amma kungiyar ta ce an rutsa da yaran kasar Yemen a cikin wata da'irar yunwa da cututuka sakamakon shekaru biyu da aka kwashe ana a yakin basasar; abin da ya lalata galibin cibiyoyin kiwon lafiya kuma ya sa aka takaita kai agajin kayan abinci da magunguna zuwa kasar abubuwan da ake matukar bukata.

Labarai masu alaka