'Nigeria na yin asarar $ 21bn saboda rashin shayar da nonon uwa'

Jarirai na kaucewa kamuwa da gudawa
Image caption Jarirai na kaucewa kamuwa da gudawa

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, Unicef, ya ce Najeriya na yin asarar $ 21bn saboda rashin shayar da nonon uwa.

Shugaban Asusun a Najeriya, Anthony Lake, ne ya bayyyana haka a wurin taro kan 'makon shayar da nonon uwa' a Abuja, babban birnin kasar.

A cewarsa, kudin da mata ke kashewa domin sayen madarar gwangwani da sauran abincin jarirai sun kai kashi 4.1 na kudin da kasar ke samu a duk shekara.

Ya kara da cewa, "Rashin shayar da jarirai nonon uwa ya sa mata na yin asara biyu: asarar rai da ta dama saboda shayarwar na kare yara daga cututtuka."

Babban jami'in na Unicef ya ce, "bai wa jariri nonon uwa a wata shida na farko yana hana shi kamuwa da gudawa da ciwon hakarkari, cutuka biyu da suka fi kashe jarirai.

Kazalika, matan da ke shayar da jariransu na tsira daga kamuwa da ciwon daji na mama da mahaifa."

Majalisar Dinkin Duniya ce ta ware wannan makon don nuna muhimmancin shayar da jarirai nonon uwa zallah.

Yayin bukukuwan makon, an kaddamar da gamayyar kasa da kasa don ganin yadda za a wayar da kan mutane su gane muhimmancin shayar da jarirai.

MDD ta ce idan da za a zuba jarin dala 4.70 don shayar da duk jariri daya, to za a samu ribar dala miliyan 300 nan gaba wanda hakan zai habaka tattaln arzikin kasar.

Hakkin mallakar hoto Jamila Gezawa
Image caption Jami'an Unicef a jihohi da dama na Najeriya sun yi ta yi wa mata bita don wayar musu da kai kan muhimmanci shayarwa
Hakkin mallakar hoto Jamila Gezawa