Majaisar dokoki ma za ta binciki zargin magudi a zaben Venezuela

Nicolas Maduro Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Maduro ya ce zaben sahihi ne kuma zargin wani kanfani daga ketare ba zai karya sahihanci ba.

Babban mai shari'a na kasar Venezuela ya kaddamar da bincike kan zargin tafka magudi a zaben sabuwar majalisar dokokin da aka gudanar a kasar ranar lahadi.

Shugaban Nicolas Maduro dai yayi fatali da zarge-zargen cewa an tafka magudi a zaben sabbin 'yan majalisar wanda ya jawo takaddama.

Yana dai mayar da martani ne ga zargin da kamfani da ya samar wa kasar da na'urorin jefa kuri'a ya yi cewa hukumar zaben kasar ta zuzuta yawan mutanen da suka fito zaben da akalla mutum miliyan daya.

Shugaban kamfanin mai suna Smart-matic da ke da mazauni a birnin London Antonio Mugica, ya ce na'urorinsa sun bayar da alkalumma na gaskiya na yawan wadanda suka yi zaben; amma sai cibiyar tattatara sakamako ta yi kari ga alkalumman.

Ita dai hukumar zaben Venezuela ta ce mutane miliyan 8 da dubu 100 ne suka jefa kuria a zaben .

Amma kamfanin dillancin labarai na Rueters ya ce samu wasu takardu daga hukumar zaben ta bayan fage da ke nuna cewa ainihin yawan wadanda suka yi zabe miliyan 3 ne da dubu 700.

'' Duk da irin matsin lambar muka fuskanta, ga wani mutum daga wani kamfani mai mazauni a London kuma yake da asusun ajiye kudinsa a Amurka yana kokari zubar da kimar wannan zabe.To ba wanda zai iya bata wannan zaben a idon mutane, saboda zabe ne da aka yi kan gaskiya, kuma aka tantance alkaluma kafin a yi da kuma bayan an yi.'' In ji shugaba Maduro.

Sai dai kakakin majalisar dokokin wadda ke hannun jam'iyyar adawa, Julio Norges, ya yi kira ga masu shigar da kara da su soma binciken zargin magudin nan take.

''Wannan majalisar za ta soma bincike, kuma muna kira ga ma'aikatar kula da lamuran jama'a da ta soma bincikar shugabannin hukumar zabe dangane da wannan al'amari mai girma. Muna kuma kiran da a yi gaskiya. Wa ya san abin da za su yi gobe? Suna son zuwa nan su gurbata mana tsarin mulki da kuma na zabe da magudi.''

A gefe guda ita ma shugabar hukumar zaben ta Venezuela Tibisay Lucena ta yi barazanar daukar matakin shari'a kan shugaban kamfanin na Smartmatic tana mai cewa zargin shaci-fadi ne kawai da aka yi da manufar zubar da kimar zaben.