Tattabaru na haddasa mutuwar aure a Indonesiya

Wacce illa hakan ke yi? Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wacce illa hakan ke yi?

Wani rahoto ya ce so da kaunar tattabaru na ci gaba da haddasa mutuwar aure a wani yanki na kasar Indonesiya.

Wani jami'i a kotun addini a Purbalingga dake tsakiyar birnin Java ya shaida wa kafar yada labarai ta Jakarta Post cewa ofishinsu ya karbi korafe-korafe da suka kai 90 a kan batun sakin aure, kari mafi yawa a idan aka kwatanta da alkaluman da suka samu guda 13 a watan Yuni.

Akawun kotun Nur Aflah, ya ce "mafiya yawan wadanda suka shigar da korafin mata ne wadanda suka rubuto korafe-korafen mutuwar aure saboda dalilai na talauci inda suka ce mazajensu na tsananin son wasan tseren tattabaru."

Wasan tseren tattabaru dai na daya daga cikin manya wasanni a kasar, inda masu gasar ke samun makudan kudade da fatan sayar da tsuntsun da ke da sauri dubban Rupia (kudin kasar).

Misis Aflah ta ce mata na cike da haushin cewar mazajen nasu na bata ilahirin lokutansu na rana tare da tattabarun nasu, a maimakon iyalansu.

Matsalar kudi ce dai ta kara ta'azzara lamarin:" a yankin na Purbalingga, akwai mata da yawa dake aiki, yayinda maza ke zaman-kashe wando.

Ta ce mafiya yawan maza kan zama 'yan 'tsere' a nan ba tana nufin 'yan tseren gudu ba, tana nufi 'yan tseren tattabaru.

Kafar yada labaran Jakarta Post ta rawaito cewar caca a kan tseren tattabaru ya haddasa rashin kudi a yankin.

Wata dake zaune a wani kauye ta shaida wa jaridar cewa duk da cewa wani lokaci mijin nata kan ba ta kudi idan ya ci cacar, to amma a mafi yawan lokuta yakan tambayeta kudin sigari.

Wasan Indiya ya rasa karkashinsa.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yaya za a shawo kan matsalar?

Wannan tamkar farfado da wasan tseren tattabaru ne da ake yi a wani yanki na kasar Indiya, wanda jaridar kasar ta rawaito cewar wasan na dab da bacewa.

Mazauna kudu maso gabashin yankin Andhra Pradesh na cewa tsohuwar al'adar mutanen yankin na dab da bacewa saboda bullowar wasanni na zamani, inda masu tattabarun ke rasa wadanda za su fafata tare.

Amma su gasar tseren tasu ta bambanta da ta Indonesiya, inda su tattabarar da ta dawo a karshe ce ake baiwa nasara, ba ta farko ba.

Masu tattabarun kan yi jira mai yawa tare da kashe kudade. Masu tseren tattabara kan kashe kusan rupee 5,000 kwatankwacin dala 78, dan ciyar da tattabarun da kuma renonsu saboda gasar, in ji jaridar Hindu.

"Wasan ya rasa karkashinsa shekaru da yawa da suka shude. Dole na hakura saboda bana samun abokin karawa" in ji wani tsohon mai tseren.

Labarai masu alaka