Ana zaben shugaban kasa a Rwanda

Magoya bayan Shugaba Kagame

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Sauran 'yan takarar dai sun ce magoyan bayansu sun fuskancin razanarwa.

Masu zabe a Rwanda na fita zuwa rumfunan zabe domin jefa kuri'a a zaben shugaban kasa wanda galibin mutane suka yi imanin zai tsawaita wa'adin mulkin Shugaba Paul Kagame.

Ana sa ran dan takarar jam'iyyar adawa Frank Habineza na jam'iyyar DGPR da kuma da takara mai zaman kansa Philippe Mpayimana su ma su fafata a zaben.

Sai dai babu daya daga cikinsu da zai iya zama barazana ga Mr. Kagame wanda ake ganin irin goyon bayan da yake da shi a cikin kasar ya isa ya ba shi gaggarumar nasara a wannnan zaben.

Ana dai yaba wa Mr. Kagame kan inganta hanyoyin cigaban tattalin arzikin Ruwanda; a yanzu kuma ya yi wanzar da zaman lafiya, da samar da tsaro da kuma ci gaba da bunkasa tattalin arziki.

Shi kuwa Mr. Habineza yayin alkawalin saukaka hanyoyin mallakar filaye da samar da gidaje ga rundunonin soji, yayin da dan takara mai zaman kansa Mr. Mpayimana ya ce zai inganta ababen more rayuwa a yankunan karkara da cibiyoyin kiwon lafiya.

An yi wa kundin tsarin mulkin Rwanda gyara ne a shekara ta 2015, abin da ya ba shugaban damar tsayawa takara domin samun wani sabon wa'adin mulki na shekaru 7 da kuma wani wa'adin na shekaru 5 har sau 2 bayan wannan.

Wannan na nufin a bisa doka zai iya ci gaba da mulki har nan shekara ta 2034.