An daure budurwa kan tura saurayinta ya kashe kansa.

Michelle Carter kenan lokacin da ake yanke masa hukunci.
Image caption Ms Carter na magana da Conrad ta waya lokacin da ya kashe kansa.

A jihar Massachusetts ta Amurka, an yankewa wata mata hukuncin daurin shekaru biyu da rabi a kurkuku saboda bai wa saurayinta kwarin gwiwar ya kashe kansa ta hanyar aike masa da sakonni wayar salula.

Michelle Carter wadda ke da shekaru 20 da haihuwa yanzu za ta yi watanni goma sha biyar a gidan yari sannan ta fuskanci dauri je-ka-gyara-halinka na shekaru biyar.

A watan Yuni na wannan shekara ne aka samu Ms Carter da laifin kisa ba da niyya ba na saurayin nata Conrad Roy, wanda ya kashe kansa a ranar 13 ga watan Yuli na shekara ta 2014.

Da farko dai ta fuskanci daurin shekaru 20 ne amma sai tawagar lauyoyinta suka nace cewa dukansu biyun ita da saurayin nata suna da tabin hankali.

Lauya mai shigar da kara ta shaida wa kotu cewa sakonni da ta aike ne suka kashe Conrad kuma ta yi hakan ne don ta kyautata tata rayuwar.

Lauyar ta nuna wa kotu wasu sakonni wayar salula da ta aike masa tana ingiza shi ya kashe kansa.

Daya daga cikin sakonni da aka karanta gaban kotun na cewa '' Ka rataye kanka, ko ka tumanyo daga wani dogon gini, ko ka daba kanka wuka ban dai sani ba akwai hanyoyi da dama da za ka iya kashe kanka.''

An shaida wa kotun cewa Conrad Roy ya kashe kansa ne a wani wurin ajiye motoci lokacin da yake dan shekaru 18, kuma a lokacin Michelle Carter tana kan waya tana ba shi kwarin gwiwar ya yi abin da ya yi niyya duk da cewa ya so ya canza shawara.

An kuma fada wa alkalin da ke shara'ar cewa daga bisani Carter ta dora alhakin mutuwarsa a kanta. Aka ce ta shaida wa wata abokiyarta cewa ''mutuwarsa laifina ne, ina iya hana shi. Kuma har ya fito daga babbar motar da ya shiga ya tsorata, amma sai na ce masa ya koma ciki yayi abin da ya yi niyya.''

Amma lauyoyinta sun ce lamarin wani abin tashin hankali ne wanda take matukar nadamar faruwarsa inda suka bukaci kotun da ta bata lokacin gyara halinta kuma a tura ta inda za a mayar da ita hayyacinta.

Da yake yanke hukuncin, Alkalin Kotun Lawrence Moniz ya yarda cewa Conrad Roy ne ya fara daukar matakai domin kashe kansa, kamar bincike hanyoyi daban-daban da mutum zai iya kashe kansa da kuma sayo abubuwan da ya yi amfani da su wajen saka wa kansa guba.

Alkalin dai ya ceyanzu Michelle za ta yi rabin wa'adin da ya yanke ma ta a gidan yari wato watanni 15 daga cikin 30 sannan ta fito ta yi zaman gyaran hali na shekaru biyar.

Iyayen Conrad sun karanto wata sanarwa a kotun yayin zaman yanke hukuncin inda suka yi kiran a yanke mata hukuncin daurin shekaru 7-12.

Mahaifinsa ya ce ya kadu sosai da ya rasa babban abokinsa domin dan nasa shi ne abokinsa na kut-da-kut; kuma ya ce Ms Carter ta yi amfani da raunin kwakwalwar dansa don ta gyara rayuwarta.