Barbashin zinare na da tasiri kan cutar daji

Cancer drugs Hakkin mallakar hoto Science Photo Library

Masu bincike daga kasar Scotland sun gano cewa amfani da barbashin zinare wajen hada maganin cutar daji ko cancer na iya kara tasirin maganin.

A wani rahoto da wata Mujallar kimiyya ta kasar Jamus ta wallafa, masana kimiyya a jami'ar (Edinburah) sun ce sun gano burbushin gwal da aka dasa a kwakwalwar wani kifi ya kara karfin magani wajen waraka.

Sun bayyana cewa barbashin zinare - wadanda ake kira "nanoparticles" - na taimakawa wajen rage tasirin maganin ciwon dajin, amma sun ce akwai sauran aiki a gaba kafin a fara gwajin maganin a kan mutane.

Labarai masu alaka