Kenya: Ana kada kuri'a a zaben shugaban kasa

Kenyans line up to vote in 2017 elections Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tun cikin dare masu son kada kuri'a suka kafa dogayen layuka a gaba da rumfunan zabe

Masu kada kuri'a sun fito domin zaben shugaban kasa da gwamnoni da kuma 'yan majalisa a Kenya.

Rahotanni sun ce akwai dogayen layuka a rumfunan zabe, inda wasu ma sun kwana akan layi suna jiran gari ya waye domin su kada kuri'unsu.

'yan kasar zasu zabi wakilai a matakai shida na gwamnatocin kasar, wanda ya fara daga matakin kananan hukumomi har zuwa na shugaban kasa.

A zaben shugaban kasa, shugaba mai ci, Uhuru Kenyatta ne zai fafata da tsohon abokin karawarsa, Raila Odinga da wasu 'yan takarar guda shida.

Mista Odinga ya nuna rashin gamsuwarsa game da ingancin tsarin amfani da fasahar zamani a wannan zaben.

Hankula sun tashi a kasar tun da aka tsinci gawar wani babban jami'in zabe na kasar mai kula da sashin fasahar zamani kwanaki kadan kafin ranar zaben.

Labarai masu alaka