Kenya: Hukumar zabe ta musanta zargin yin kutse a na'urarta

Wani mai zanga-zanga a Kenya

Asalin hoton, ROBERTO SCHMIDT

Bayanan hoto,

Ana fargabar barkewar rikicin bayan zabe a kasar irin na shekara ta 2017.

Hukumar zaben kasar Kenya wato IEBC ta ce babu wani kutse da aka yi wa na'urorinta daga ciki ko waje a kowane lokaci a yayin zabukan.

Shugaban hukumar ne dai ya fitar da wata sanarwa domin mayar da martani ga ikrarin da dan takatar shugaban kasa na jam'iyyar adawa Raila Odinga ya yi.

Mr. Odinga - babban abokin karawar Shugaban Uhuru Kenyatta a zaben - ya yi zargin cewa masu kutse sun kutsa ciki na'urar da ke tattara sakamako suka sassauya sakamakon.

A yanzu ana kan tantance jimillar kuri'un da kowane dan takara ya samu na karshe, amma a bisa sakamakon farko-farko da aka samu, shugaba mai ci Uhuru Kenyatta na kan gaba da rata mai dama.

A halin yanzu dai hukumar zaben na bincike kan sakamakon farko da ta riga ta sanar domin ganin ko akwai wani choge.

An dai samu zanga-zanga da kuma dauki-ba-dadi da 'yansanda nan da can a unguwannin marasa galihu inda 'yan adawa ke da goyon baya.

Amma dai ana fatan Kenya za ta iya kaucewa fadawa cikin rikici idan aka tantance sakamakon da kyau ta yadda kowa zai yi na'am da shi, kuma idan 'yan adawa suka zabi su kalubanci sakamakon a kotu maimakon a kan titi.