Gudun hijira: Nigeria da Kamaru sun kulla sabuwar yarjejeniya

'Yan gudun hijrar Nigeria a Kamaru

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Kamaru dai fna argabar cewa akwai 'yan Boko Haram sake a cikin 'yan gudun hijirar.

Gwamnatocin Nigeria da Kamaru sun sake rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya dangane da yadda yafi dacewa a mai do tare da kula da dubban 'yan Nigeria din da suka arce zuwa Kamaru din domin gujewa rikicin Boko Haram.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira da Majalisar Dinki Duniya ce dai ta shiga tsakani wajen kulla wannan yarjejeniyar wadda aka rattaba wa hannu ranar Alhamis a Abuja babban birnin Najeriya.

A cikin wata hira da BBC, Ministan lamurran cikin gida na Nigeria, Abdurrahman Dambazzau ya ce akwai wata hukuma da suka kafa nan take da za ta sake duba tsarin da ya kamata a bi wajen mai do da 'yan gudun hijirar.

''Ana so a duba cewar duk wanda za a mayar inda ya fito, za a mayar da shi ne saboda yana son mai da shi, na biyu kuma za kare mutucinsa yayin mayar da shi din, za a duba lafiyarsa da rayuwarsa gaba daya wajen mayar da shin;'' inji ministan.

Shi ma dai takwaransa na kasar Kamaru Rene Emmanuel Sadi ya shaida wa BBCn cewa akwai akalla 'yan gudun hijirar Nigeria 58,000 a sansanin Minawawo kawai baya ga wadanda ke fakewa a gidajen 'yan uwa da aboka arziki.

A watan Maris ma kasashen biyu tare da hukumar ta UNHCR sun rattaba hannun kan irin wannan yarjejeniyar game da 'yan gudun hijirar Nigeria; amma sai aka rika samun kace-nace game da aiki da sharrudanta.