Ana dab da sanar da wanda ya lashe zaben shugaban kasar Kenya

Wasu jaridun kasar Kenya

Asalin hoton, Ronald Grant

Bayanan hoto,

Sakamakon farko ya nuna Kenyatta ya samu 55% na kuri'un ya yin da Odinga ya samu 44%

Nan gaba kadan a yau Jumu'a ne ake sa ran sanar da sakamakon karshe na zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar Kenya tun ranar Talata.

Sakamakon farko dai ya nuna cewa shugaba mai ci Uhuru Kenyatta ya sha gaban babban abokin hamayyarsa Raila Odinga da yawan kuri'u.

Amma magoya bayan Mr. Odinga sun wallafa nasu sakamakon da ya nuna cewa gogan nasu ne kan gaba.

Sun ce an yi kutse a cikin na'urorin hukumar zaben kasar aka murde sakamakon don hana Mr. Odinga samun galaba.

Sai dai hukumar zaben kasar ta bayyana ikirarin na 'yan adawa a matsayin maras tushe kuma wanda ya keta doka.

Masu sa ido kan zaben na kasa-da-kasa sun bayyana cewa zaben kasar Kenyar sahihi ne.