Nigeria: Za a 'hukunta' masu kalaman batanci

Ministan lamuran cikin gidan na Nigeria tare ba babban jami'an shige da fice Hakkin mallakar hoto BBC HAUSA
Image caption Yanzu an fi musayar kalaman nuna kiyyayar ne tsakani al'ummar Igbo ta kudu maso gabas da Hausa/fulani na arewa.

Gwamnatin Najeriya ta ce ta soma shirye-shiryen aike wa da wata bukata zuwa ga majalisar dokokin kasar dake neman yin dokar da za ta fayyace irin hukuncin da za a yi kan wadanda aka samu na furta kalaman kiyayya ga wani jinsi a kasar.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin zaman tankiya ke karuwa tsakanin a kabilu da addinai da kuma yankunan kasar daban-daban, inda har wasu ke kiran da a raba ta ko a sake mata fasali.

Ministan lamurran cikin gida Abdurrahman Dambazau ya ce ana neman kafa wannan dokar ne domin a halin yanzu babu wani tanadi a kundin tsarin mulkin kasar na hukunta masu furta irin wadannan kalaman.

''Yanzu mun tura (daftarin bukatar) zuwa ga ministan shari'a, zai duba, idan ya duba, ya ga komai ya kamalla zai tura zuwa ga majalisar dokoki don a kafa doka,'' in ji ministan a yayin wata zantawa da manema labarai.

Ya ce wannan dokar ita ce za ta fayyace irin laifin da wanda ya furta kalaman nuna kiyayya ga wani jinsi a kasar ya aikata da kuma irin hukuncin da za a yi masa.