Kun san gwagwarmayar da India ta yi kafin samun 'yanci?

Al'ummar Kasar India ke daga tuta suna murnar zagayowar ranar samun 'yancin kasarsu Hakkin mallakar hoto Getty Images

A ranar 15 ga watan Agusta ne kasar Indiya ta yi bikin murnar samun 'yancin kai daga Turawan Mulkin Mallaka na Ingila, wanda aka kusan shafe shekara 300 ana gwagwarmayar, domin Turawa sun shiga kasar ne tun a farkon karni na 17.

Indiya dai ta samu 'yancin kai bayan fadi tashin da wasu 'yan gwagwarmaya suka shafe tsawon lokaci suna yi.

Mutane irin su Gopal Krishna Gokhale, su ne suka fara kaddamar da kiraye-kiraye ga al'umma kasar da su fito su bayyana bukatarsu ta samun 'yancin kai, lamarin da ya kai ga asarar rayuka da dukiyoyi.

Kasar Indiya ta gamu da dumbin kalubale kafin ta kai ga samun 'yanci kai, domin tun a kusan shekarar 1929, jam'iyyar National Congress ta ayyana ranar 26 ga watan Janairu a matsayin ranar samun 'yancin kasa, inda suka rika gabatar da taruka a boye, gudun kar su bayyana su gamu da fushin hukumar kasar Ingila.

Haka aka rika tafiya har zuwa lokacin da Mohandas Karamchand Ghandi ya dawo kasar, sakamakon kiransa da manyan 'yan siyasar kasar suka yi na ya zo domin ya taimaka musu a kawo karshen mulkin mallaka.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Zuwan Mahatma Ghandi ne ya sauya tafiyar siyasar kasar, kasancewarsa mutum mai tsananin son zaman lafiya da daidaito ta fuskar zamantakewa, ya shiga gaba don tabbatar da cewa Turawa sun daina matsawa Indiyawa ta fuskar haraji, da bauta da sauran su.

Sai dai yunkurin da 'yan jam'iyyar National Congress suka fara na ganin Indiya a kan kanta ta samu 'yanci, ya samu tasgaro a lokacin da yankin Pakistan mai rinjayen Musulmai ta ki amincewa da zama karkashin Indiya, ta kuma yi yunkurin ballewa kwata-kwata.

Yunkurin Pakistan ne ya raba hankulan Turawa, suka rasa ta inda za su fara, saboda haka aka jibge sojoji a tsakanin Pakistan da Indiya domin ganin an dakile 'yan fafutukar, wanda a dalilin haka sama da mutum miliyan daya ne suka rasa rayukansu.

Kafin daga bisani Turawa su ayyana Pakistan din a matsayin 'yantacciyar kasa ranar 14 ga watan Agusta, 1947, wato ta girmi Indiya da kwana daya.

Duk da alkawura da Gwamnan Indiya Clement Attlee ya yi, na cewar za a bai wa kasar 'yanci a watan Yunin 1948, manyan 'yan siyasa sun ki amincewa da bukatarsa, inda a daren ranar 15 (14 Agusta) da misali karfe 11 na dare, suka hadu domin bayyana matsayarsu kan gwagwarmayar da ake ta yi ta samun 'yanci.

Cikin wadanda suka halarci zaman akwai Shugaban Kasa Rajendra Prasad, da wasu manyan kungiyoyi na mata.

Gaba daya mahalarta taron sun mika kansu don ganin an fitar da kasar daga kangin talauci da fatara da kuma bautarwa.

Firai minista Jawaharlal Nehru, ya yi jawabi mai ratsa a zuciya a taron, inda ya rika karfafa gwiwa kan muhimmanci tashi domin a kwaci 'yancin kai.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Haka kuwa aka yi, washegari dole Turawa suka ayyana Indiya a matsayin 'yantacciyar kasa don kaucewa asarar rayukan da aka kwashe watanni ana yi.

Amma duk da haka kasar ba ta fara aiki da Kundin Tsari na kashin kai ba sai 26 ga watan Janairun 1950.

Bayan samun 'yancin ne, al'umma kasar suka rika kiran sunan Mahatma Ghandi da jinjina masa sakamakon irin gudunmuwar da ya bayar a nasarar da aka mu.

Wasu na bayyana sunansa a matsayin sabon shugaba.

Sai dai a nasa bangaren, ya nuna sam ba shi da sha'awar mulki, sai ma kira da ya yi ga al'ummar kasar mabiya addinin Musulunci, mabiya addinin Hindu da mabiya addinin Sikh da su yi hakuri, su zauna lafiya da juna.

Daga bisani aka nada Jawaharlal Nehru Firai minista, sai kuma Lord Mountbatten a matsayin Gwamna kafin kundin tsarin mulkin kasar ya fara aiki.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A bangaren Pakistan kuma aka rantsar da Muhammad Ali Jinnah a matsayin Gwamna.

Tattalin arzikin Indiya kullum yana habaka ta hanyar Kimiyya da Fasaha da Likitanci da kuma Fina-finai.

A bangaren fim kadai, duk shekara masana'antar Bollywood tana samar da kudin shiga a kalla Dala Bilyan takwas, ko fiye da haka. Baya ga dimbin ayyukan yi da take samar wa matasa.

Labarai masu alaka